Jerin gwamnonin Najeriya 11 da suka kamu da cutar Coronavirus
Bayan watanni 11 da bullar cutar Coronavirus a Najeriya, Akalla gwamnoni 11 sun kamu da cutar.
Adadin wadanda suka kamu da cutar kawo yammacin Talata sun zarce 120,000 bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya wato NCDC.
Cutar ta yadu cikin mutane daban-daban wanda ya hada da yan siyasa, malaman addini, manyan yan kasuwa, Likitoci, Malaman jinya, da sauran su.
Ga jerin gwamnonin bakwai da Korona ta harba:
1. Bala Mohammed: Ya kwashe kwanaki 15 a killace
Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ne gwamnan farko da ya kamu da cutar COVID-19.
A ranar 24 ga Maris, hadiminsa, Mukhtar Gidado, ya saki jawabin cewa gwamnan ya killace kansa. Amma ranar 9 ga Afrilu gwamna ya warke
2. Nasir El-Rufa'i: Ya kwashe makonni 3 a killace
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ne gwamna na biyu da cutar a Najeriya. Hakazalika shine mutumin farko da ya kamu da cutar a jiharsa.
A faifan bidiyon da ya saki ranar 28 ga Maris, gwamnan ya sanar hakan.
3. Seyi Makinde: Ya warke cikin kasa da mako daya
A ranar 30 ga Maris, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da cewa ya killace kansa bayan kamuwa da cutar Coronavirus.
4. Ikeazu Ikpeazu: Ya warke bayan kimanin wata daya
Gwamnan jihar Abia, Ikpeazu ya sanar da cewa ya kamu da cutar ranar 8 ga Yuni, 2020.
Bayan kimanin wata daya, gwamnan ya warke ranar Asabar, 4 ga watan Yuli.
5. Ifeanyi Okowa
Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya kamu da cutar Corona tare da matarsa, Edith, da daya cikin 'yayansa mata.
6. Rotimi Akeredolu
A ranar Talata, gwamnan jihar Ondo, ya sanar da cewa ya kamu da cutar COVID-19. Amma Akeredolu ya bayyana cewa duk da cewa yana killace, ba mika ragamar mulki hannun mataimakinsa ba.
7. David Umahi
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya kamu a da cutar watanni shida da suka wuce.
Hakazalika ya sanar da cewa ya wasu daga cikin hadimansa sun kamu da cutar.
8. Kayode Fayemi
Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kamu da cutar a watan Yuli 2020.
9. Babajide Sanwo-Olu
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya kamu da cutar Korona ana gab da bikin Kirismeti a Disamban, 2020.
Bayan yan kwanaki a killace a samu lafiya.
10. Simon Lalong
Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, tare da wasu hadimansa sun kamu da muguwar cutar a watan Disamba.
11. Samuel Ortom
A ranar 27 ga Junairu 2021, sakataren yada labaran gwamnan jihar Benue, ya sanar da kamuwar maigidansa da cutar Korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng