Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40

Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40

- Kafintan da matansa hudu suka haihu a cikin makonni uku ya bayyana irin murnar da yake ciki

- Ya ce a halin yanzu yana da yara 13 amma burinsa shine haifar a kalla yara 40 tun yana karami

- Ya ce Allah ne ke ciyarwa ba dan Adam ba, hakan ne yasa ya aura mata hudu kuma za su haifa masa yara

Nura Walwala Magaji kafinta ne mai shekaru 36 daga gundumar Zango ta karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi.

Ya ce yana alfahari da yadda ya haifa yara 13, maza 10 sai mata 3. Yana fatan cika burinsa na yarinta inda yake son haifar 'ya'ya a kalla 40.

Kamar yadda jaridar Community Vanguard ta wallafa, Magaji yana da mata hudu kuma kowacce ta haihu a cikin makonni uku. Ya ce kula da su ba zai zama matsala ba domin Allah ne ke kula da yara.

A yayin zantawa da jaridar Leadership, ya ce, "'Ya'ya kyauta ne daga Allah kuma ina farin ciki saboda matana sun haihu a cikin makonni uku. Maza uku, mace daya.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna

Kafinta da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40
Kafinta da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40. Hoto daga community.vanguardngr.com
Asali: UGC

"Auren mata da yawa a jinina ne. A takaice na gaji hakan ne daga bangaren kakannina na wurin uwa da uba.

"Mahaifin mahaifiyata ya aura mata hudu, haka shima mahaifin mahaifina. Tabbas wasu za su ce abun dariya ne amma ina matukar alfahari da wannan nasarar.

"Tun ina yaro nake rokon Allah da ya albarkace ni da a kalla 'ya'ya 40, lamarin da ke baiwa jama'a dariya.

"Kun san kowa da ra'ayinsa kuma baka iya yi wa wani dole ya bi ra'ayinka. Allah yace kula da iyali shi ke yi ba mutum ba. Allah ne kuma ya bada umarnin mu aura mata biyu, ko uku ko kuma hudu in dai za a yi adalci garesu.

"Babban kuskure ne mutum yayi tsarin iyali saboda yana tsoron talauci. Yarana 13, maza 10, mata 3.

"Tara daga ciki duk sun shiga makarantun boko kuma kamar yadda kuke gani ga Alaramma can yana koyar da su haddar Qur'ani," yace.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano ta rushe gidan da masu garkuwa da mutane ke boye mutane

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Kaduna ta amince da bude makarantun gaba da sakandare na jihar a ranar Litinin, 25 ga watan Janairun 2021 a fadin jihar baki daya.

Amma kuma ta ja kunnen dukkan hukumomin makarantun da su kasance masu kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona da jihar ta Gindaya, Daily Trust ta tabbatar da hakan.

A wata takardar da ma'aikatar ilimi ta jihar ta fitar kuma ta samu sa hannun babbar sakatariyar ma'aikatar, Phoebi Sukai Yayi, an bayyana cewa wannan amincewar ta biyo bayan tura kungiyar dubawa tare da tantancewa dukkan makarantun gaba da sakandare na jihar, wadanda suka tabbatar da cewa makarantun sun shirya kuma sun kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar annobar korona a fadin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: