Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata

Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata

- Wata budurwa ta bayyana yadda ake gane mace tagari a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

- Kamar yadda Icon Babe mai amfani da suna @Glad_Peace ta wallafa, dole ne mace tagari tayi shiru idan namiji yana magana

- Babu shakka wallafarta ta tada kura inda masu amfani da kafar suka dinga bayyana nasu ra'ayin

Al'amuran soyayya da alaka tsakanin mata da maza ba abubuwa bane da masu amfani da kafar sada zumuntar zamani ke yin shiru idan aka tsokano.

Zamani ya zo da sauyi daban-daban domin yanzu ba a kallon mata a matsayin masu karamin tunani a yayin soyayya.

Hakan ne kuwa ya bai wa jama'a mamaki bayan da budurwa mai amfani da sunan Icon Babe a Twitter ta yi magana a kan yadda ake gane mace tagari.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar

Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata
Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata. Hoto daga @Glad_peace
Source: Twitter

Budurwar ta gigita Twitter bayan ta ce mace tagari ita ce wacce miji zai yi magana amma tayi shiru saboda nuna girmamawa. Idan kuwa budurwa ce, toh tabbas ta cancanci a aureta.

Ta wallafa: "Manta da soyayya Inna, idan ba za ki iya shiru ba yayin da namiji ke magana, toh baki cancanci a aureki ba."

Babu jimawa jama'a suka dinga yi mata raddi tare da caccakar ta.

Aries cewa yayi: "A gaskiya idan tana da hankali, shiru mace take yi idan namiji yana magana. Na kan cewa mata kada su aura namiji idan ba za su iya girmama shi ba."

Morounkejimi kuwa ta yadda da cewa dole ne kowa ya girmama kowa ba wai mace ce kadai za ta girmama namiji ba.

Ariella ta ce ba kowacce ba mace bace take so a aureta ba.

Nikky ta bi ra'ayin Ariella inda tace ba tazo duniya don kawai ta zama mace tagari ba.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna

A wani labari na daban, wani bidiyo mai cike da bada mamaki ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani.

A bidiyon, an saurayi yana dukan budurwarsa yayin da abokansa suke taya shi jibgarta. Kamar yadda aka gano kuma bidiyon ya bayyana, budurwar ta ci amanar saurayin nata ne da wani saurayin na daban.

A bidiyon, an ga budurwar tana ihun neman dauki yayin da kattin maza ke ta dukanta. Babu shakka bidiyon ya samu kushe tare da Allah wadai daga jama'a da suka kalla.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel