2023: Jama'a sun yi wa 'yan majalisar Kogi wankin babban bargo
- Gangamin kamfen da 'yan majalisar jihar Edo suka yi wa Gwamna Bello ya janyo suka kala-kala
- 'Yan majalisar jihar Edo sun ziyarci jihohin Ebonyi, Filato da Kogi inda suke neman goyon bayan takwarorinsu a kan takarar da Bello ke son yi
- Jama'a sun caccakesu ganin cewa Kogi jiha ce da bata da kayan more rayuwa kuma bata iya biyan kudin albashin ma'aikata
An saka 'yan majalisar jihar Kogi gaba da caccaka bayan zagayen jihohi da suka yi suna nemawa gwamna Yahaya Bello goyon baya daga jama'a domin fitowa takarar shugaban kasa a 2023.
'Yan majalisar da suka ziyarci Filato, Ebonyi da jihar Kogi, sun yi kira ga takwarorinsu da su goyi bayan Gwamna Bello idan 2023 ta iso.
DUBA WANNAN: Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, tunda har yanzu arewa ta tsakiya bata fitar da dan takarar shugaban kasa ba, akwai bukatar APC ta mika tikitinta ga Bello domin yayi takarar.
A yayin ziyara a jihar Ebonyi, kakakin majalisar Kogi, Matthew Kolawole ya yi kira ga takwarorinsa da su sanar da David Umahi cewa yayi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa yana son fitowa takarar shugabancin kasa sannan kuma ya goyi bayan Bello.
Babu kakkautawa aka dinga jin martani bayan 'yan majalisar sun gama zagayen. Da yawan 'yan jihar Kogi sun zargi Gwamna Bello da tura 'yan majalisar don su yi masa kamfen.
KU KARANTA: Babu wanda ya bawa makiyaya wa'adin barin Kudu maso Yamma, in ji NGF
Idris Miliki Abdul, daraktan kungiyar masu rajin kare dan Adam da sasanci ya soki wannan gangamin da 'yan majalisar suka yi zuwa jihohi.
Ya ce wannan majalisar ta jihar za a iya kiranta da majalisa mafi muni da suka taba samu a jihar Kogi.
Hakazalika, shugaban jam'iyyar SDP, Mukhtar Attimah, ya ce kakakin majalisar jihar ba'a kawai yake wa jama'a domin daga shi har takwarorinsa na jihar ba da gaske suke ba.
Ya yi mamakin yadda jihar da basu da kayan more rayuwa kuma basu iya biyan albashin ma'aikata amma 'yan majalisar sun yi shiru.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ngng
Asali: Legit.ng