Gwamnan jihar Kwara ya kafa dokar daina baiwa Bukola Saraki kudin fansho

Gwamnan jihar Kwara ya kafa dokar daina baiwa Bukola Saraki kudin fansho

- Bayan fitittikan Saraki da mabiyansa daga gwamnati, gwamnan Kwara ya sake wani babban canji

- Gwamnan ya shiga jerin gwamnonin da suke da ra'ayi daina biyan tsaffin gwamnoni fansho

- Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya rattafa hannu kan irin dokar

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a ranar Talata, ya rattafa hannu kan dokar daina baiwa tsaffin gwamnoni da mataimakansu na jihar kudin fansho.

A watan Nuwamba, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sanar da niyyar canza dokar jihar saboda gwamnatin ba za ta iya cigaba da biyan tsaffin gwamnoni makudan kudi ba.

Sai ya gabatar da kudirinsa gaban majalisar dokokin jihar.

Wadanda suka amfana da wannan doka sune tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda yayi mulki tsakanin 2003 da 2011, sannan Abdulfatah Ahmed da yayi tsakanin 2011 da 2019.

Saraki ne ya kafa dokar bada makudan kudin matsayin fansho lokacin da yake gwamna a 2011.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Yakubu Danladi-Shehu da wasu mambobinsa sun halarci bikin rattafa hannu kan dokar.

Mr Danladi-Shehu ya ce al'ummar jihar sun yi na'am da wannan doka.

Duk a bikin, gwamnan ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2021.

KU DUBA: Saura Kiris allurar Covid 19 ta iso Nigeria, Boss Mustapha

Gwamnan jihar Kwara ya kafa dokar daina baiwa Bukola Saraki da mataimakinsa kudin fansho
Gwamnan jihar Kwara ya kafa dokar daina baiwa Bukola Saraki da mataimakinsa kudin fansho hoto: Kwara
Source: Twitter

DUBA NAN: Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho

A wani labarin, ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, gwamnatin jihar Imo ta yi kaca-kaca da tsohon gwamna, Sanata Rochas Owelle Okorocha.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnatin Imo ta ce Sanata Rochas Okorocha ‘bai da kunya.’

Jawabin gwamnatin Imo ya fito ne ta bakin Kwamishinan yada labarai da dabaru, Declan Emelumba, ya ce tsohon gwamnan ya yi facaka da baitul-mali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel