Tsohon Gwamna Rochas Okorocha bai da kunya, inji Gwamnatin Jihar Imo

Tsohon Gwamna Rochas Okorocha bai da kunya, inji Gwamnatin Jihar Imo

- Hope Uzodinma ya ragargaji Rochas Okorocha, ya ce Sanatan bai da kunya

- Gwamnan ya ce ba a taba mummunar gwamnati a Imo kamar ta Okorocha ba

- Declan Emelumba ya ce Okorocha yana kan hanyarsa na tafiya gidan yari

A ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, gwamnatin jihar Imo ta yi kaca-kaca da tsohon gwamna, Sanata Rochas Owelle Okorocha.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnatin Imo ta ce Sanata Rochas Okorocha ‘bai da kunya.’

Jawabin gwamnatin Imo ya fito ne ta bakin Kwamishinan yada labarai da dabaru, Declan Emelumba, ya ce tsohon gwamnan ya yi facaka da baitul-mali.

Kwamishinan ya ce: “Bai da kunya kuma ba zai iya gyara kuskuren da ya yi na kin neman afuwar jama’a na jagorantar mafi munin gwamnatin da aka yi tun da aka kirkiri Imo a 1976.”

KU KARANTA: EFCC, SPIP sun taba cafke Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma

“Gwamnatinsa annoba ce da ta gagara, mafi muni tun da aka kirkiri jihar Imo. Ba abin mamaki bane da kwamitin bincike ya gano kwangilar N106b sun bi iska a mulkinsa.”

Mista Declan Emelumba ya cigaba da cewa: “Ba don gwamnati tana so a bi doka ba, da yanzu (Rochas Okorocha) ya zama ‘dan takarar gidan kurkuku.”

“Me zai koya wa Uzodinma, yadda za a saci kudin jiha? Gina hanyoyin Sin? Maida gwamnatin jiha ta zama mallakar mutum? Yadda za ayi mulkin dangi?

A cewar Kwamishinan na Uzodinma, wasu wadanda tsohuwar gwamnatin jihar ta karbe masu filaye, suna jin haushin kin kama Rochas Okorocha da aka yi.

KU KARANTA: Gwamnan Imo ya kai wa Buhari ziyara a Aso Villa

Tsohon Gwamna Rochas Okorocha bai da kunya, inji Gwamnatin Jihar Imo
Gwamnan Jihar Imo da Shugaban kasa Hoto: Twitter Daga: @Govhopeuzodinma
Asali: Facebook

Emelumba ya yi wannan bambami ne a matsayin raddi ga ofishin Okorocha bayan ya fito ya na zargin mai gidansa da boye dukiyar gwamnati a wani dakin adana.

A makon nan ne Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom ya fada wa magoya-bayansa cewa su daina buga masa gangar neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Ganin cewa jama’a na ta kiran Ortom ya fito takara a 2023, gwamnan ya maida masu martani.

Mai girma gwamna Samuel Ortom ya ce a yanzu, bai da sha’awar takarar Shugaban Najeriya a zabe mai zuwa, don haka ya ce a daina tsumbula shi a siyasar 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel