Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari

Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari

- Honarabul Ben Igbakpa, mamba a majalisar wakilai, ya caccaki ministan yada labarai, Lai Mohammed

- A cewar dan majalisar, kalaman Lai Mohammed na matukat bashi mamaki duk lokacin da ya ke sauraronsa

- Igbakpa ya zargi Lai Mohammed da rashin sanin banbanci tsakanin yada labarai da sharara karya da furta shirme

Mamba a majalisar wakilai daga mazabar Ethiope, jihar Delta, Honarabul Ben Igbakpa, ya caccaki ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, tare da yin kira gare shi ya daina shararawa 'yan Nigeria karya yayin gudanar da aikinsa.

Dan majalisar ya bayyana kalaman Lai Mohammed na kare shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a matsayin abin kunya.

A cewar dan majalisar, Lai Mohammed "karya kawai ya ke shararawa tare da kara yawan matsalolin gwamnatinsu duk lokacin da ka saurari kalamansa.

KARANTA: Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto)

Da ya ke magana da jaridar Vanguard a ranar Litinin, dan majalisar bayyana cewa; "ina mamakin yadda jama'a ke manta cewa ba'a dawwama a gwamnati, watarana dole mutum zai bar ofis.

"Na tabbata da ace ba'a cikin gwamnati yake ba shi ma ba zai ke furta irin wadannan Kalaman da yake yi yanzu ba.

Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari
Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari
Asali: Twitter

"Kare shugaban kasa ba kishin kasa bane, tsayawa tare da sauran jama'a da kundin tsarin mulki shine kishin kasa, amma shi kullum kalamansa na shirme ne da rashin kishin kasa.

"Ba zan manta lokacin da Jonathan ke kan mulki ba, yadda ya dinga caccakarsa, shi yasa yanzu yake borin kunya.

KARANTA: Hoton mace bakar fata zai maye gurbin na tsohon shugaban Amurka a jikin Dala

"Ya bar aikinsa na Ministan yada labarai ya koma shugaban yada farfaganda, ya gaza gamsar da 'yan Nigeria cewa yana yin aikin da aka nada shi; wato sanar da su gaskiyar al'amuran gwamnati.

"Amma shi a wurin Lai Mohammed, aikin ministan yada labarai shine sharara karya, watakila saboda babu wani abu da zai nuna wanda gwamnatinsu ta yi wa kasa," a cewar dan majalisar.

A makon jiya ne Legit.ng ta rawaito cewa fitaccen masanin adabi da rubutun zube a yaren Turanci, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana cewa ya yafewa Amurkawan da suka zabi tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Farfesa Soyinka, mai lambar yabo ta kwazo na musamman a fagen iliminsa, ya bayyana tsohon shugaba Trump a matsayin mutum mai kyamar bakar fata da nunawa bakin haure kyama.

A shekarar 2016 ne Farfesa Soyinka ya yayyaga katin shaidar zama dan kasar Amurka mai daraja ta musamman saboda kawai Amurkawa sun zabi Trump.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel