Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto)

Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto)

- Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta yi bajakolin wasu dumbin 'yan bindiga da tarin makamansu da aka kama

- A karshen mako ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umartar a kara tsananta yaki da 'yan ta'adda a jihar Zamfara

- Jihohin arewa da suka hada da Katsina, Sokoto, da Zamfara suna fama da hare-haren 'yan bindiga

Hukumar yan sanda ta yi holin wani mutum mai suna Haruna Yusuf, ɗan jamhuriyar Nijar, wanda ake zargin da safara tare da sayar da makamai ga masu garkuwa mutane.

Kwamishinan yan sandan jihar Katsina, Sunusi Buba, ya ce, malam Yusuf dan shekara 47, mazaunin Maduru dake ƙaramar hukumar Mani ta jihar Katsina, shine ke jagorantar shigo da makamai ga yan ta'addan da suka addabi Katsina da Zamfara.

A cewar kwamishina Buba, an kama malam Yusuf ne tare da ya'yan cikinsa guda biyu; Ibrahim mai shekara 20 da Shuaibu mai shekara 18, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

KARANTA: Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo

Sauran waɗanda aka yi holinsu sun haɗa da Haruna Yusuf mai shekara 47, Haruna Adamu mai shekara 35 sai kuma Auwal Abubakar mai shekaru 28.

Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto)
Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto) @Premiumtimesng
Source: Twitter

Sauran sun haɗa da, Sani Ibrahim, 20; Yusufa Muhammadu, 28; Abubakar Muhammadu, 26; Abdullahi Dabo, 28; Murtala Ado, 20, Sani Muhammad, 29; sai kuma Umar Bello, 28; dukkansu daga ƙauyen Natsinta, Kandamau, Maradin a jamhuriyar Niger.

KARANTA: Farfesa Jega ya amsa tambaya akan kokarin gwamnatin Buhari tun bayan hawa mulki

Rundunar 'yan sandan ta samu gagarumar nasara a yaki da ta'addanci a jihar Katsina bayan ta yi bajakolin dumbin 'yan bindiga da tarin makamansu da suka shiga hannu.

A jerin wasu hotuna da rundunar 'yan sanda ta wallafa, an ga 'yan bindiga da dama tare da dumbin miyagun makamansu yayin da aka yi holinsu a Ofishin 'yan sanda.

Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke kashe jama'a a Nigeria

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu dalilai hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin baya kungiyar Boko Haram a cikin wannan shekarar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel