Hoton mace bakar fata zai maye gurbin na tsohon shugaban Amurka a jikin Dala

Hoton mace bakar fata zai maye gurbin na tsohon shugaban Amurka a jikin Dala

- Sabon shugaban Amurka, Joe Biden, ya farfado da yunkurin kasar na saka hoton mace bakar fata a jikin takardar Dala

- An yi tsammanin cewa tun a shekarar 2020 Amurka za ta fara buga takardun Dala da hoton matar mai suna Harriet Tubma

- Tubman za ta maye gurbin tsohon kasar Amurka, Andrew Jackson, a jikin takardar Dala ashirin

Harriet Tubman, wata bakar fata da aka haifa a matsayin baiwa a shekarar 1820 za ta shiga tarihin kasar Amurka a matsayin mace ta farko da za'a fara saka hotonta a jikin takardar Dala.

BBC ta rawaito cewa tun a cikin shekarar 2020 aka saka ran kasar Amurka za ta fara buga takardun Dala da hoton Tubman.

Tubman, 'yar gwagwarmayar yaki da cinikin bayi, za ta maye gurbin tsohon shugaban kasar Amurka, Andrew Jackson, wanda tarihi ya nuna ya taba mallakar bayi a baya.

A cewar rahoton da BBC ta wallafa, tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya saka siyasa a batun fara buga takardun Dala da hotunan Tubman.

KARANTA: Katsina: 'Yan sanda sun yi caraf da Haruna Yusuf, jagoran safarar bindigu daga Nijar (Hoto)

Sai dai, yanzu, sabon shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya sake farfado da yunkurin, kamar yadda kakakin fadar gwamnatin kasar Amurka, Jes Paki, ta sanar.

Joe Biden: Amurka za ta saka hoton mace 'yar Afrika a jikin takardar Dala
Joe Biden: Amurka za ta saka hoton mace 'yar Afrika a jikin takardar Dala @BBC
Asali: Twitter

KARANTA: Haba, Malam Sani: Auren dattijo da matashiyar budurwa ya yamutsa hazo, ya girgiza yanar gizo

A cewar kakakin, nan bada dadewa ba kasar Amurka za ta fara buga takardun Dala 20 da hotunan Tubman.

Tubman Za ta kasance mace, bakar-fata, ta farko da hoton ta ya samu irin wannan karramawa.

A makon jiya ne Legit.ng ta rawaito cewa fitaccen masanin adabi da rubutun zube a yaren Turanci, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana cewa ya yafewa Amurkawan da suka zabi tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Farfesa Soyinka, mai lambar yabo ta kwazo na musamman a fagen iliminsa, ya bayyana tsohon shugaba Trump a matsayin mutum mai kyamar bakar fata da nunawa bakin haure kyama.

A shekarar 2016 ne Farfesa Soyinka ya yayyaga katin shaidar zama dan kasar Amurka mai daraja ta musamman saboda kawai Amurkawa sun zabi Trump.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel