Farfesa Wole Soyinka: Na yafewa Amurkawan da suka zabi Trump, yanzu zan iya komawa Amurka
- Farfesa Wole Soyinka ya ce ya yafewa Amurkawa kuskuren da suka yi na zaben Donald Trump shekaru hudu da suka wuce
- Bayan Amurkawa sun zabi Trump a 20216, Farfesa Soyinka ya yayyaga katin shaidar zama dan kasa mai daraja da Amurka ta bashi
- Fitaccen Farfesan ya bayyana Trump a matsayin mai nuna wariyar launin fata da kiyayyar bakin haure
Fitaccen masanin adabi da rubutun zube a yaren Turanci, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana cewa ya yafewa Amurkawan da suka zabi tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Farfesa Soyinka, mai lambar yabo ta kwazo na musamman a fagen iliminsa, ya bayyana tsohon shugaba Trump a matsayin mutum mai kyamar bakar fata da nunawa bakin haure kyama.
Babban Malamin ya furta wadannan kalamai ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin din 'Arise' a ranar Laraba, kamar yadda Punch ta rawaito.
A shekarar 2016 ne Farfesa Soyinka ya yayyaga katin shaidar zama dan kasar Amurka mai daraja ta musamman saboda kawai Amurkawa sun zabi Trump.
A cewar Farfesa Soyinka, babu bukatar ya sabunta katin da ya yayyaga saboda yana iya ziyartar Amurka ko babu shi.
Da yake nuna gutsurarrun takardun katin, Farfesa Soyinka ya bayyana cewa yanzu Amurka ta tsaftace kanta bayan kawo karshen mulkin Trump.
"Na ji dadi cewa ina cikin wadanda suka fito suka nuna cewa Amurka ta yi kuskure a baya kuma yanzu ga shi sun gyara kuskurensu.
"Yanzu zan iya cewa na koma cikin al'ummar da na nesanta kaina daga garesu shekaru hudu da suka gabata, kuma na ji dadin hakan, amma ba zan sabunta katin da na yaga ba. Zan cigaba da ziyartar kasa, zan shiga na kuma fita a matsayin bako," a cewar Farfesa Soyinka.
Farfesa Soyinka ya bayyana cewa ya shiga damuwa bayan zaben Trump a 2016 saboda akwai dumbin 'yan Nigeria da ke zaune a kasar Amurka.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng