Yanzu yanzu: Gobara ta tashi a fitaccen kasuwar Legas

Yanzu yanzu: Gobara ta tashi a fitaccen kasuwar Legas

- Gobara ta tashi a kasuwar Somolu da ke jihar Legas a safiyar ranar Talata

- A yayin da al'ummar unguwar ke kokarin tsira da kayyakinsu, bata gari suna ta fasa shaguna suna sata

- Al'ummar unguwar suna kira da 'yan kwana kwana da yan sanda da sauran jami'an da abin ya shafa su kai musu dauki

An yi asarar kadarori masu yawa sakamakon gobarar da ta tashi a safiyar ranar Talata, kuma har yanzu tana ci a kasuwar Somolu da ke jihar Legas.

A misalin karfe 7 na safiyar yau, jami'an kwana kwana ba su riga sun isa inda gobarar ke ci ba domin kai dauki a cewar rahoton da The Vanguard ta wallafa.

Yanzu yanzu: Gobara ta tashi a fitaccen kasuwar Legas
Yanzu yanzu: Gobara ta tashi a fitaccen kasuwar Legas. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An cafke uba da ƴaƴan sa biyu a cikin gungun 'yan bindigan Katsina

A yanzu ba a san takamammen dalilin da ya janyo gobarar ba a yayin da al'ummar da ke kusa da kasuwar ke kokarin tsira da rayukansu da kadarorinsu.

A cewar wata majiya, bata gari suna amfani da damar domin sace kayayyakin shagunan yan kasuwar ta Somolu.

KU KARANTA: Wata mata ta sheƙawa kishiyarta tafasasshen ruwan zafi a Kano

Mazauna unguwar suna kira da jami'an rundunar 'yan sanda da Hukumar kashe gobara ta Jihar Legas da Hukumar bada Agajin Gaggawa na JIhar Legas, LASEMA, su kawo musu dauki cikin gagagawa.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel