An cafke uba da ƴaƴan sa biyu a cikin gungun 'yan bindigan Katsina
- An yi baja kolin yan tawaye a hedikwatar rundunar yan sandan Jihar Katsina tare da makaman su
- Daga cikin wanda rundunar tayi baja koli akwai wani uba da yayan sa biyu da ake zargi da safarar makamai ga yan bindigar da ke daji
- An kama manyan makamai da dama a hannun yan bindigar tare da bubura bakwai, wanda aka gabatar lokacin baja kolin
Wani uba da biyu daga cikin yayan shi na daga cikin mutum 16 da rundunar yan sandan Katsina tayi baja kolin su a hedikwatar yan sandan jihar bisa zargin ayyukan yan bindiga da kuma safarar makamai ga yan bindigar.
An gano manyan bindigu masu sarrafa kansu guda biyu, bindiga kirar LAR, da kuma harsashin baro jirgi guda 200 daga yan ta'addar kuma an gabatar da makaman lokacin baja kolin.
DUBA WANNAN: Buhari ya amince a dauki matasa masu shaidar karatu 30,000 ayyuka
Dillalin makamai, Haruna Yusuf, dan shekara 47, da yayan sa biyu Shuaibu Haruna, dan shekara 18, Murtala Haruna, dan shekara 20, da dan dan uwan sa Ibrahim Salisu, mai shekara 20, duk daga kauyen Sawarya, karamar hukumar Kaita da ke Jihar Katsina na cikin wanda aka yi baja kolin.
Daga cikin wanda aka baja kolin akwai yan kasar Nijar biyu, Ibrahim Dabo, mai shekaru 19, da Umar Bello, dan shekara 28.
Kwamishinan yan sandan Katsina, Sunusi Buba, wanda yayi wa yan jarida bayani lokacin baja kolin yan ta'addar da kuma gabatar da makaman, bai bayyana lokacin da aka kama wanda ake zargin ba.
Kwamishinan, ya alakanta kama su da gano makaman a matsayin "kwarewar aiki".
KU KARANTA: Ka hukunta shugabannin APC da suka aikata laifuka, PDP ta roki Biden
Ya ce, "sanadiyar kwarewar aiki, rundunar mu ta bibiyi wani, Lawan Zayyana, na miji, dan shekara 35 dan kauyen Muduru, karamar hukumar Mani a Jihar Katsina, mashahurin dan bindiga mai kuma safarar makamai ga yan bindigar da ke daji.
"Bayan gudanar bincike, an kama wanda ake zargin bayan an fafata barin wuta wanda ya janyo kama masu tallafa masa, Haruna Yusuf, mai shekara 47 daga kauyen Sawarya a karamar hukumar Kaita da ke Jihar Katsina, Haruna Adamu, dan shekara 35, da Auwal Abubakar mai shekara 28 duk daga kauyen Muduru, karamar hukumar Mani da ke Jihar Katsina."
"Bugu da kari, Haruna Yusuf ya amsa cewa shi ne shugaban tawagar kuma ana shigo masa da makamai daga Kasar Nijar shi kuma yana kaiwa Lawan Zayyana, Haruna Adamu da Auwal Abubakar wanda su kuma suke kai wa yan bindiga a daji. Ya kuma amsa cewa ya siyar da makamai fiye da dubu goma ga yan bindigar da ke daji."
"Sannan, Haruna Adamu da Auwal Abubakar sun tabbatar da cewa sun kai makamai da dama ga yan bindigar Gurbi da Da-Magaji a Jihar Zamfara."
Kwamishinan ya bayyana cewa an gano makamai masu yawa tare da yan ta'addan, har ma da babura bakwai.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng