An kama ɗan sandan bogi da tabar 'wiwi' a Legas

An kama ɗan sandan bogi da tabar 'wiwi' a Legas

- Yan sandan jihar Legas sun damke wani dan sandan bogi, David Omoruyi da tabar wiwi

- Wanda aka kama, Omoruyi, tare da katin shaidar dan sanda na bogi ya ce shi ba dan sanda bane

- Kwamishinan yan sandan Legas ya bada umurnin a mika shi ga sashin masu binciken manyan laifuka wato CID

'Yan sandan Area E Command a Festac jihar Legas sun kama wani David Omoruyi, dan shekara 37 mazaunin No 4 Job Street Afromedia, Oto-Awori LCDA saboda laifin yi wa yan sanda sojan gona, Vanguard ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jihar, Olamuyiwa Adejobi, ya ce an kama Omoruyi dauke da katin shaidan dan sanda na bogi da kuma wani ganye da ake zargin tabar wiwi mai nauyin kilogram 30.

An kama dan sandan bogi da wiwi a Legas
An kama dan sandan bogi da wiwi a Legas. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

"An gano Omoruyi dauke da wasu jakunnan tabar wiwi a kasuwar Alaba, Ojo da ke Legas yana gudu tare da abokansa kafin a kama shi.

"Omuruyi ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne mai mukamin saja da ke aiki tare da Mopol 49, a jihar Legas amma a yayin da ake masa tambayoyi a caji ofis ya amsa cewa shi dan sandan bogi ne," in ji Adejobi.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

Ya amsa cewa yana amfani da takardan shaidan na bogi domin safarar miyagun kwayoyi zuwa duk inda ya ke so a jihar.

Adejobi ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ya umurci DPO na yankuna su kara mayar da hankali don inganta tsaro a jihar.

KU KARANTA: Jerin manyan kyaututuka masu tsada 10 da aka yi wa Donald Trump

"Odumosu ya umurci a mika wanda ake zargin zuwa sashin masu binciken manyan laifuka da ke Panti Yaba domin zurfafa bincike.

"Odumosu ya kuma umurci jami'an yan sanda su kamo sauran wadanda suka gudu domin su fuskanci hukunci.

"Har wa yau, Odumosu ya gargadi al'umma su rika taimakawa 'yan sanda da bayyanai masu amfani domin su rika gudanar da ayyukansu yadda ya kamata," in ji Adejobi.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel