Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

Al'amuran siyasa a kasar Amurka sun dauki wani sabon salon tarihin yayin da Joe Biden ya zama shugaba mafi yawan shekaru a tarihin Amurka.

Dan jami'iyyar Democrat din, da aka rantsar ranar Laraba, 20 ga Janairu, a matsayin shugaban Amurka na 46. Abun ban sha'awa ya zama na 15 a jerin mataimakan shugaban kasa da suka dare shugabancin kasar Amurka.

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Asali: Getty Images

Legit.ng ta tattaro jerin mataimakan shugabannin Amurka da suka dare shugabancin Kasar, ko dai bayan mutuwar na kan karagar ko ta har zabe ko kuma murabus.

1. John Adams

Adam shine mataimakin shugaba George Washington. An zabe shi bayan Washington yayi murabus daga shugabancin Kasar. Shi ne shugaban Amurka na farko da ya bar fadar White House.

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka. Hoto: Hulton Archive
Asali: Getty Images

2. Thomas Jefferson

Jefferson ne mataimakin shugaban kasar Amurka na biyu. Shi ne mataimakin shugaban Amurka kafin yayi takara da uban gidan nasa, John Adams kuma yayi nasara a 1800.

3. Martin Van Buren

Buren ne ya kafa jami'iyyar Democratic. Yayi wa Andrew Jackson mataimakin shugaban kafin ya zama shugaban Amurka na takwas.

4. John Tyler

Tyler ne mataimakin shugaban Amurka na 10 a 1841 zamanin shugaba William Henry Harrison. Ya zama shugaban Amurka na 10 bayan rasuwar Harrison.

5. Millard Fillmore

Fillmore, dan jami'iyyar Whig mataimakin tsohon shugaba Zachary Taylor. Ya zama shugaban Amurka bayan mutuwar Taylor wanda ya na 13 a jerin shugabannin Kasar.

6. Andrew Johnson

Johnson ne mataimakin shugaba Abraham Lincoln. Ya zama shugaban Amurka na 17 bayan an kashe Lincoln.

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka. Hoto: Hulton Archive
Asali: Getty Images

7. Chester Arthur

Shi ne mataimakin shugaban Amurka na 20 karkashin James Garfield. Kamar dai Johnson, Arthur ya zama shugaban Amurka na 21 bayan an kashe Garfield.

8. Theodore Roosevelt

Roosevelt Wanda aka fi sani da T.R ne shugaban Amurka na 26. Dan jami'iyyar Republican ne da ya yi wa William McKinley mataiki.

9. Calvin Coolidge

Coolidge, dan jami'iyyar Republican shi ne mataimakin shugaba Warren G. Harding. Ya zama shugaban Amurka na 30 bayan rasuwar Harding.

10. Harry Truman

Truman ya zama shugaban Amurka na 33 bayan kasancewar sa mataimaki na 34. Ya karbi ragamar bayan rasuwar Franklin D. Roosevelt. An sake zaben Truman tazarce.

11. Lyndon Johnson

Johnson ya zama shugaba na 36 bayan kasancewar sa mataimakin shugaban kasar Amurka na 37, ya zama shugaban kasa bayan an kashe Kennedy, wanda ya yiwa mataimakin.

12. Richard Nixon

Nixon, dan jami'iyyar Republican shine mataimakin shugaban Amurka na 36 lokacin shugaba Dwight Eisenhower, bayan shekara takwas, ya zama shugaban Amurka na 37.

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka. Hoto: Don Carl STEFFEN/Gamma-Rapho
Asali: Getty Images

13. Gerald Ford

Ford ne na 40 kuma mataimakin Nixon. Ya zama shugaban Amurka na 38 bayan Nixon yayi murabus.

14. George H. W. Bush

Bush ya yi wa Ronald Reagan mataimaki kafin ya zama shugaban Amurka na 41 bayan gajeren lokacin da wanda ya gada ya shafe.

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka. Hoto: Shepard Sherbell
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

15. Joseph R Biden

Sabon shugaban Amurka ne na karshe a jadawalin, ya yi wa shugaba Barack Obama mataimaki. Biden ne mataimaki na 15 wanda ya samu damar zama shugaban Amurka

Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka
Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka. Hoto: Chip Somodevilla
Asali: Getty Images

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel