Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji

Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji

- Yan Boko Haram sun yi ikirarin kwace makaman jami'an tsaro

- Daga cikin abubuwan da sukay ikirarin kwatowa akwai iga da harsasai

Kungiyar masu tada kayar bayan Boko Haram a ranar Asabar ta saki sabon bidiyo dake nuna igwa, makamai da harsasan da mambobin kungiyar suka kwace a cikin dajin Sambisa, jihar Borno.

Daya daga cikin yan ta'addan wanda yayi jawabi a bidiyo mai tsawon mintuna 4.15 yayi jawabi kan artabun da sukayi da Sojojin a dajin Sambisa ranar Juma'a, HumAngle ta ruwaito.

Wata motar Igwa Vickers Mk.3 Eagle, harsasai igwa masu yawa da harsasan bindiga.

Wannan na faruwa a lokacin da dakarun Sojin Najeriya suka kaddamar da atisayen Operation Tura Takai Bango inda suka farautar yan ta'addan ISWAO a dajin Alagarno- yankin Timbuktu.

Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji
Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji Hoto: humangle.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnati ta yi rabon N619.34bn a matsayin kason FAAC a Disamban bara

Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji
Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji Hoto: humangle.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta gaza cika alkawarin da ta yiwa yan Najeriya, Solomon Dalung

A wani labarin kuwa, mayakan Boko Haram a Nasarawa sun kashe sojoji tara a yayin wani aikin ceto a dajin da ke hanyar Mararaba-Udege a jihar Nasarawa wanda ke hada jihar da Otukpo Oweto a jihar Benue.

Sojojin da aka kashe wanda wani jami’i Felix Kura, dan asalin jihar Benuwe ya jagoranta zuwa dajin sun hada da Iliya Kefas, Bati Yakubu da wasu kananan jami’an da ba za a iya tantance sunayensu nan take ba.

Jaridar The Nation ta tattaro daga majiya cewa jami’an da aka kashe suna kan aikin fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka sace yan asalin jihar da dama tare da tsare su daga dajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel