Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa

Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa

- Yan ta'addan Boko Haram sun halaka jami'an sojoji tara a jihar Nasarawa

- Hakan ya faru ne a kwanton baunar da maharan suka kai wa sojin a yayinda suke aikin ceto wasu mutane da suka yi garkuwa da su a dajin da ke hanyar Mararaba-Udege

- Sai dai sojin ma sun yi nasarar halaka yan ta'adda biyar

Mayakan Boko Haram a Nasarawa sun kashe sojoji tara a yayin wani aikin ceto a dajin da ke hanyar Mararaba-Udege a jihar Nasarawa wanda ke hada jihar da Otukpo Oweto a jihar Benue.

Sojojin da aka kashe wanda wani jami’i Felix Kura, dan asalin jihar Benuwe ya jagoranta zuwa dajin sun hada da Iliya Kefas, Bati Yakubu da wasu kananan jami’an da ba za a iya tantance sunayensu nan take ba.

Jaridar The Nation ta tattaro daga majiya cewa jami’an da aka kashe suna kan aikin fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka sace yan asalin jihar da dama tare da tsare su daga dajin.

Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa
Abun bakin ciki: Yan Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Makiyaya sun fayyace mani komai game da ta'addancin da yadda za a kawo karshen shi, in ji Sheikh Gumi

Aikin ya yi sanadiyar mutuwar kimanin yan Boko Haram biyar kafin yan ta’addan suka sha karfin sojojin da makamansu da ya fi nasu karfi.

A cewar rahotanni, sojojin da aka kashe sun kasane na bataliya 177, sansanin Shitu da ke Keffi, jihar Nasarawa.

“Suna karo da kwanton baunar sannan sai suka fahimci cewa an ci karfinsu, an ce sai Kura ya fada ma abokan aikinsa da su tsere.

"Mahukuntan Bataliya ta 117 sun sanar da dangin sojojin da aka kashe makomarsu sannan kuma an aika sakonni zuwa hedkwatar," in ji wata majiya.

Amma wata majiya a barikin ta shaida wa jaridar The Nation: “A zahiri mun rasa sojoji tara a wannan aikin ba bakwai ba, abin takaici ne matuka amma wannan shi ne mafi girman sadaukarwar jami’in soja.

KU KARANTA KUMA: Kotun koli ta yi watsi da bukatar iyalan Abacha na mallakar kudaden da ya sata

"A yanzu haka muna hada gwiwa da runduna ta musamman a hedikwatar sojojin Najeriya da ke karamar hukumar Doma ta jihar don karfafawa tare da kaddamar da daukar fansa, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, dole ne mu mamaye su sannan mu tabbatar mun fatattake su gaba daya."

A gefe guda, mun ji cewa wasu mutane biyu da ake zaton yan fashi da makami ne sun shiga hannu a yankin Zangon Kataf da ke Kaduna.

Ana zargin Abdulhameed Abubakar Bala da Abubakar Abdulhameed Garba da hannu a wasu jerin hare-hare da aka kai al'umman Gora Gan, Damkasuwa, Zonzon da Kwaku.

A yanzu haka suna hannun sojoji yayinda ake gudanar da bincike.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel