Gwamnati ta yi rabon N619.34bn a matsayin kason FAAC a Disamban bara

Gwamnati ta yi rabon N619.34bn a matsayin kason FAAC a Disamban bara

- A watan Disamba, an raba Naira biliyan 619 daga asusun tarayya na FAAC

- Gwamnatin tarayya ta tashi da kaso mafi tsoka, ta samu Naira biliyan 218.3

- Gwamnoni 36 da kananan hukumomi sun tashi da kusan Naira biliyan 400

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an raba Naira biliyan 619.343 daga asusun tarayya na FAAC a watan Disamban shekarar da ta wuce, 2020.

Rahoton ya bayyana cewa Naira biliyan 600 ne abin da gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka samu a matsayin kason watan jiya.

Daga cikin wannan kudi, gwamnatin tarayya ta tashi da Naira biliyan 218.3, sannan an raba Naira biliyan 178.3 tsakanin gwamnonin jihohi 36.

Sai kuma kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin Najeriya sun tashi da Naira biliyan 131.8.

KU KARANTA: NEC ta yi zama a kan COVID-19, Gwamnoni sun nesanta kansu da Yahaya Bello

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnati Ta Tanadi N470bn Don Karawa Malaman Jami'a Albashi Da Gyara Jami'a

Sauran jihohi da ke da arzikin danyen mai sun samu karin Naira biliyan 31.8. A dokar kasa, ana biyan duk jihohin da ake hako mansu karin 13%.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta biya jihohi da makamantansu kudinsu da ke hannunta, Naira biliyan 59.1

Abin da gwamnatin kasar ta iya samu a watan jiyan ya gaza, don haka aka hada da wasu Naira biliyan 10 da ke cikin asusun kudin canjin kasar waje.

Bayanan da aka fitar bayan taron rabon FAAC ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta samu fiye da Naira biliyan 170 daga kudin harajin VAT a Disamba.

KU KARANTA: Ana son sanin kadarorin da Shugaban INEC da ‘Ya ‘yansa su ka mallaka

Gwamnati ta yi rabon N619.34bn a matsayin kason FAAC a Disamban bara
Ministar kudin Najeriya, Zainab Ahmed Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

An ba gwamnatin tarayya Naira biliyan 23.9 daga kason na harajin VAT, bayan haka, jihohi da kananan hukumomi sun samu Naira biliyan 79.6 da 55.7.

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

An biya kwastam da hukumar FIRS ladar N6.8b, an ware wa ma’aikatar NEDC N5.1bn daga cikin kudin.

Dazu kun ji cewaHukumar SUBEB ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65 da aka dauka aiki ba tare da an bi ka'idoji da matakai ba.

Hukumar dillancin labarai na NANS ta fitar da wannan rahoto bayan an gudanar da wani bincike.

Wani jami'in binciken hukumar SUBEB, Tandat Kutama, ya shaida wa manema labarai wannan. Ya ce an kori wadannan mutane daga bakin aikinsu gaba daya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel