Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Shehun Dikwa, Dr Abba Tor Masta II rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Shehun Dikwa, Dr Abba Tor Masta II rasuwa

- Allah ya yi wa Shehun Dikwa, Mai Martaba Dakta Abba Tor Masta II rasuwa a jihar Borno

- Marigayin ya rasu ne a safiyar ranar yau Asabar bayan fama da rashin lafiya kuma za a yi jana'ziarsa a yau

- Gwamnan Borno, Babagana Zulum, Shehun Borno, Dakta Abubakar El-Kanemi da sauran sarakuna suna hanyar zuwa hallartar jana'izar

Sarki mai sanda mai daraja ta daya a Borno, Shehun Dikwa, Mai Martaba Dakta Abba Tor Masta II, ya rasu a cewar majiyoyi daga iyalansa, The Vanguard ta ruwaito.

Majiyoyin sun bayyana cewa sarkin wanda shine na biyu a jihar bayan Shehun Borno ya rasu ne a safiyar ranar Asabar bayan fama da wata rashin lafiya da ba a bayyana irinta ba.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Shehun Dikwa, Dr Abba Tor Masta II rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Shehun Dikwa, Dr Abba Tor Masta II rasuwa. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: An fatattaki Sarkin Fulanin Oyo da iyalansa daga gidansa, an ƙone motocinsa 11

Kazalika, majiyoyin sun bayyana cewa za a yi wa Shehun jana'iza a yau a Maiduguri bisa koyarwar addinin musulunci duk da cewa gwamnan jihar Babagana Zulum da mataimakinsa, Umar Usman Kadafur da wasu manyan mutane a jihar suna karamar hukumar Biu domin bikin nadin sabon sarki Mai Martaba Umar Mustapha Aliyu bayan rasuwar mahaifinsa a bara.

Tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff ne ya nada Alhaji Abba Tor Shehu Masta II sarki a watan Maris na 2020 a matsayin Shehun sabon masarautar Dikwa da aka kirkira.

KU KARANTA: Jerin sunaye: Joe Biden da wasu mataimakan shugaban ƙasa 14 da suka zama shugabannin ƙasa a Amurka

A lokacin da aka hada wannan rahoton, Gwamna Zulum da Shehun Borno, Dakta Abubakar El-Kanemi da sauran sarakuna da suka tafi halartar nadin sarkin Biu suna hanyarsu ta komawa Maiduguri domin hallartar jana'izar.

Alhaji Abba Tor Shehu Masta II da ne ga marigayi Shehu Masta II da aka fi sani da Shehu Masta Kyarimi wanda aka nada a matsayin Shehun Dikwa a 1973 amma daga bisani ya koma Bama a 1942 bisa umurnin turawan mulkin mallaka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel