Hotuna: An fatattaki Sarkin Fulanin Oyo da iyalansa daga gidansa, an ƙone motocinsa 11
- An kone gida da motoccin sarkin fulanin Oyo, Saliu Abdulkadir a daren ranar Juma'a
- Sarkin fulanin ya ce yan sanda da sauran jami'an tsaro suna kallo aka kone gidansa
- Abdulkadir ya ce shi da iyalansa sun koma cikin daji duk da cewa an raunata wasu yaransa
Wasu 'yan banga da ke ikirarin kare kabilar Yarabawa sun cinna wuta a gidan Sarkin Fulanin Oyo, Alhaji Saliu Abdulkadir a daren ranar Juma'a, SaharaReporters ta ruwaito.
Abdulkadir ya shaidawa SaharaReporters a Ibadan cewa an fatattake shi da matansa da yaransa daga gidansu sannan an kone motoccinsa 11 yayin korarsu.
DUBA WANNAN: Yanzu haka: Ƴan Boko Haram na can sun kai hari a garinsu Gwamna Zulum a Borno
Ya ce duk da tabbacin kariya da rundunar yan sanda da al'ummar jihar suka bashi, an kone gidansa a gaban jami'an tsaro.
Ya ce, "A yanzu da na ke magana, muna daji. An kone motoccin mu kimanin 11. Wasu daga cikin yara na sun samu rauni kuma muna neman yadda zamu kai su asibiti. Yara ne sun tsere daga gidajensu sun shiga daji. Muna bukatar gwamnati ta taimake mu. Yan sanda da Operation Bust da sauran jami'an tsaro suna nan lokacin da ake cinna wa gida na wuta."
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Ibrahim Jiji, shima ya tabbatar da afkuwar lamarin ga wakilin majiyar Legit.ng a wayar tarho.
KU KARANTA: Jerin manyan kyaututuka masu tsada 10 da aka yi wa Donald Trump
"Kamar yadda muka saba fadi, ba dukkan fulani ne bata gari ba. Akwai na gari a cikin mu. Me za a kira wannan? Wannan mutumin dattijo ne kuma duba yadda aka kore shi daga gidansa. Muna bukatar gwamnati ta dauki mataki," in ji shi
Sunday Igboho, wani mai fafutikan kafa Jamhuriyar Odudua, a ranar Juma'a ya ziyarci unguwannin Fulani domin tabbatar da sun fice daga jihar bayan cikar wa'adin kwana bakwai da aka basu a makon da ta gabata.
Tuni dai babban sufetan 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya bada umurnin a kamo Igboho.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng