Babu uban da ya isa ya kori Fulani daga dazukan jihar Ondo, shugaban Miyetti Allah

Babu uban da ya isa ya kori Fulani daga dazukan jihar Ondo, shugaban Miyetti Allah

- Wa'adin da gwamnan jihar Ondo ya baiwa makiyaya su fita daga dazukan jihar na gabatowa

- Shugaba Miyetti Allah ya umurci Fulanin dake daji kada su saurari maganar gwamnan

- Fadar shugaban kasa ta jaddada cewa gwamnan bai yi daidai ba

Shugaban uwar kungiyar Miyetti Allah Kautal Hoore, Bello Bodejo, ya ce babu wanda ya isa kori makiyaya dake dazukan jihar Ondo.

A hirar da yayi da jaridar The Sun, Bodejo, ya ce makiyayan ba zasu bi umurnin Akeredolu ba saboda ba shi hakkin bada wannan umurni, saboda Fulani sun fi shekaru 250 suna kiwo a wajen.

Ya ce makiyaya basu bukatar izinin kowa kafin suyi amfani da wani daji muddin suna da bukatar hakan.

"Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, bai da wannan hakkin barazana ga mutanenmu. Mutane, har da yan Fulani sun zabeshi kafin ya zama gwamna, saboda haka kamata yayi ya zama gwamnan kowa," yace.

"Fulani sun kasance cikin dazukan da yake magana kai tun kan a haifesa; sun kasance a wajen tun shekaru 250 da suka gabata."

"Bayan kwashe shekaru a wajen kuma kashin shanu sun maishe da kasar wajen iya noma, mutane suka je wajen suna noma, sai su zo suna ikirarin cewa shanunmu na lalata musu gona."

"Za mu kai gwamnan kotu kuma mu bukaci a hanashi aiwatar da barazanarsa. Amma duk da haka, babu uban da ya isa ya kori makiyaya daga jihar Ondo."

"Babu makiyayin da zai bi umurnin gwamnan. Makiyayan ba zasu fita daga dajin Ondo ba; babu inda zasu je. Ba zamu bi umurnin gwamnan ba; kundin tsarin mulkin Najeriya kawai zamu bi," ya kara

KU KARANTA: Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa

Babu uban da ya isa ya kori Fulani daga dazukan jihar Ondo, shugaban Miyetti Allah
Babu uban da ya isa ya kori Fulani daga dazukan jihar Ondo, shugaban Miyetti Allah
Source: Depositphotos

DUBA NAN: Kaiwa Fulani hari a kasar Yarabawa na iya haddasa wani yakin basasa

A wani labarin mai alaka, yayinda wa'adin da gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya baiwa Fulani su bar dazukan jihar ke kusantowa, ya bada umurnin daukan sabbin jami'an Amotekun da yawa.

Kwamandan hukumar na jihar, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da hakan a hira da jaridar TheCable ranar Juma'a.

"Gwamnan ya bada umurnin daukan sabbin jami'ai da yawa. Dauka kyauta ne. za ku iya dauka foma a shafin yanar gizonmu," Adeleye yace.

Hakazalika, kwamishanan labaran jihar, Donald Ojogo, ya tabbatar da hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel