Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa

Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa

- Gwamnan Ondo ya tsaya kan bakansa na koran Fulani makiyaya daga dazukan jiharsa

- Fadar shugaban kasa ta bayyana masa cewa abinda yake niyyan yi ba zai yiwu ba

- Yanzu da alamun gwamnan na kokarin fito na fito da gwamnatin tarayya

Yayinda wa'adin da gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya baiwa Fulani su bar dazukan jihar ke kusantowa, ya bada umurnin daukan sabbin jami'an Amotekun da yawa.

Kwamandan hukumar na jihar, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da hakan a hira da jaridar TheCable ranar Juma'a.

"Gwamnan ya bada umurnin daukan sabbin jami'ai da yawa. Dauka kyauta ne. za ku iya dauka foma a shafin yanar gizonmu," Adeleye yace.

Hakazalika, kwamishanan labaran jihar, Donald Ojogo, ya tabbatar da hakan.

KU DUBA: Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC

Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa
Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa
Source: Twitter

KU KARANTA: Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soki umarnin gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na korar makiya daga dazukan Jihar Ondo.

Premium Times ta ruwaito umarnin Akeredolu a ranar Litinin, a wani mataki na dakile garkuwa da mutane a jihar.

"Cikin kwana 7, makiyaya su bar dazukan jihar nan, daga yau zuwa Litinin 18 ga Janairun 2021," a cewar gwamnan.

A martanin ta ranar Talata, fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Mr Akeredolu, babban lauya, "ba za a tsammaci ya kori dubban makiyayan da rayuwar su ta dogara da jihar ba bisa yan ta'addan da suka mamaye daji ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel