Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa

Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa

- Duk da gargadin da gwamnan jihar yayi masa, Sunday Igboho ya dira garin Fulani don koransu daga kasar Yarabawa

- Mai rajin kasar Oduduwan ya yi alhinin yadda Fulani ke garkuwa da mutane a yankin

- A ziyararsa, ya ce ba yaki ta kawo shi ba amma don gargadinsu kawai

Wani mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo Igboho, a ranar Juma'a ya dira Igangan, karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo kamar yadda yayi alkawari.

Duk da cewa bai yaki Fulanin dake zaune a garin ba kamar yadda akayi yada a kafafen sada zumunta, ya jaddada cewa Fulani mazauna jihar su tattara inasu-inasu su bar jihar da kasar Yarabawa muddin aka cigaba da garkuwa da mutane.

A makon jiya, Igboho ya kai ziyara unguwar Fulani dake Igangan, inda ya basu kwanaki bakwai su fita daga garin.

Ya tuhumci yan kabilar Fulani dake yankin da laifin garkuwa da mutane, kashe-kashe, da wasu ayyulan alfasha a garin.

Adeyemo wanda yayi jawabi da yaren Yarabanci ya ce abinda yan kabilar Yoruba ke tsoro shine kada wasu bare su kwace musu gari.

KU KARANTA: Yan Boko Haram na gangami a jihata, Gwamnan Nasarawa ga Buhari

Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa
Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa Hoto: @thenationnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsaro: Sarakunan gargajiya na yi min zagon kasa, Matawalle ya caccaki sarkin Anka

Yace: "Ba zai yiwu Fulani su kwace mana gari ba. Garinmu mallakinmu ne kuma ba zamu yarda wani ya kwace ba. Wasu na yi mana barazana amma ba zamu ji tsoronsu ba."

"Ga Fulanin dake nan, ba yaki muke da su ba, idan zasu zauna da mu cikin lafiya. Tsoronmu shine kada su kwace mana gari, suna garkuwa da mu kuma suna kashe mu."

"Za mu koresu daga kasarmu idan suka cigaba da sace mana mutane. Ina tabbatarwa al'ummar Yoruba, musamman mazauna jihar Oyo cewa babu wani tsoro. Ba a jihar Oyo kadai zamu fitittiki Fulani ba, amma dukkan jihohin Yoruba."

A bangare guda, gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya kai kuka kan yadda yan ta'addan Boko Haram suka fara gangami a jiharsa suna cin karensu ba babbaka.

Gwamnan yayi jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan zamansa da shugaba Buhari a fadarsa ta Aso Villa, dake birnin tarayya Abuja, rahoton The Nation.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel