Kaiwa Fulani hari a kasar Yarabawa na iya haddasa wani yakin basasa

Kaiwa Fulani hari a kasar Yarabawa na iya haddasa wani yakin basasa

- Kungiyar ACF na tsoron abinda ke faruwa yanzu a kudu maso yamma na iya haddasa wani sabon yaki

- Wani jagoran matasa ya umurci Fulani Makiyaya su fita daga kasar Yarbawa

- Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin kama wannan matashi

Kungiyar kare mutuncin Arewacin Najeriya, Arewa Consultative Forum (ACF), ta bukaci gwamnatin kudu maso yammacin Najeriya da gwamnatin tarayya su dakatad da hare-haren da ake kaiwa Fulani da yankinsu.

ACF ta yi gargadin cew idan ba'a hana kai wadannan hare-hare kan Fulani ba, zai iya haddasa ramuwar gayya a Arewa kuma za'a iya maimata yakin basasan 1967, The Nation ta ruwaito.

A jawabin da kungiyar ta saki ranar Asabar, ACF ta ce abinda ya haddasa yakin 1967 shine hare-haren da aka rika kaiwa juna a kudu da Arewa kuma irin haka ya fara faruwa yanzu a kudu maso yamma.

Wani sashen jawabin yace: "Kungiyar ACF da safen nan ta samu labarin harin da matasan Yarbawa suka kai kan Alhaji Saliu Abdulkadir, sarkin Fulanin jihar Oyo."

"Abin damuwan shine an sanar da jami'an tsaro yiwuwan haka amma basu dau wani mataki ba lokacin da ake kai harin."

"ACF na bayyana damuwarta kan wannan abu kuma tana kira ga gwamnatin tarayya da na jihohin kudu maso yamma su tashi tsaye ko kuma wani mugun tarzoma da ka iya rikita kasar nan ya tashi."

"Munyi waiwayen cewa yakin basasan ya fara ne daga hare-hare irin wannan."

"Wajibi ne gwamnatocin su tashi tsaye kada tarihi ya maimaita kansa."

DUBA NAN: Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC

Kaiwa Fulani hari a kasar Yarabawa na iya haddasa wani yakin basasa
Kaiwa Fulani hari a kasar Yarabawa na iya haddasa wani yakin basasa Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa

Mun kawo muku cewa wani mai rajin kafa kasar Oduduwa, Sunday Adeyemo Igboho, a ranar Juma'a ya dira Igangan, karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo kamar yadda yayi alkawari.

Duk da cewa bai yaki Fulanin dake zaune a garin ba kamar yadda akayi yada a kafafen sada zumunta, ya jaddada cewa Fulani mazauna jihar su tattara inasu-inasu su bar jihar da kasar Yarabawa muddin aka cigaba da garkuwa da mutane.

A makon jiya, Igboho ya kai ziyara unguwar Fulani dake Igangan, inda ya basu kwanaki bakwai su fita daga garin.

Ya tuhumci yan kabilar Fulani dake yankin da laifin garkuwa da mutane, kashe-kashe, da wasu ayyulan alfasha a garin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng