COVID-19: Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje

COVID-19: Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje

- Gwamna Ganduje ya yi barazanar kulle kasuwanni idan ba ayi hattara ba

- Ganduje ya yi alhinin waiwayen annobar Korona na biyu inda ta hallaka mutane 17

- Gwamnan ya ce cutar yanzu ta fi tsanani fiye da lokacin bullarta ta farko amma duk da haka ba zasu kulle makarantun jihar ba

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce ba zai kyautatu a rufe makarantu domin hana yaduwar cutar Korona ba a jiharsa.

A cewar jawabin da sakataren yada labaran Ganduje, Abba Anwar, ya saki, ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a wata ganawa da kungiyar malaman Najeriya (NUT).

Ganduje ya ce rufe makarantu zai janyo koma baya a harkar ilimi kuma hakan ba zai hana yara kamuwa da cutar Koronan ba.

"Akwai bukatar yaki da annobar, amma mutane su fahimci illar wasu abubuwan da sukeyi," yace.

"Matsalan ba rufe makarantu bane. Idan ka rufe makarantu, wani hadarin ne, saboda idan kuka kulle makarantu da niyyar hana dalibai kamuwa da COVID-19, wannan cutar na iya kamasu a gidajensu."

"Rufe makarantu zai zama koma baya ga daliban da kuma harkar ilimi. Shi yasa muka ki umurtan malamai su zauna a gida, sabanin ma'aikatan gwamnati da muka umurta suyi zamansu a gida."

A cewar NAN, gwamnan ya ce jihar za ta samar da wasu hanyoyi na daban domin dakile yaduwar cutar.

KU DUBA: Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

COVID-19: Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje
COVID-19: Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje Hoto: Maikatanga
Source: Twitter

KU KARANTA: Wa'adin korar Fulani daga dazukan Ondo: Gwamnan ya bada umurnin daukan jami'an Amotekun da yawa

A wani labarin kuwa, shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa amfanin barin yara su koma makaranta ya rinjayi tsoron kamuwa da cutar Korona.

Ihekweazu ya bayyana hakan a taron kungiyar likitocin yaran Najeriya watau (PAN) ranar Juma'a a jihar Legas, The Cable ta ruwaito.

Ihekweazu ya ce lallai ya yi na'am da shawaran bude makarantu.

Diraktan ya ce Najeriya ta fi kowace kasa yawan adadin yara maras zuwa makaranta a duniya, kuma cigaba da ajiyesu a gida babban illa ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel