Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC

Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC

- Gwamnatin tarayya ta amince a bude makarantu tun ranar 18 ga Junairu 2021

- Wasu gwamnoni har yanzu sun cigaba da rufe makarantun saboda cutar Korona

- Daliban makarantun firamare, sakandare, da jami'o'i sun kwace kimanin watanni 10 a gida

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana cewa amfanin barin yara su koma makaranta ya rinjayi tsoron kamuwa da cutar Korona.

Ihekweazu ya bayyana hakan a taron kungiyar likitocin yaran Najeriya watau (PAN) ranar Juma'a a jihar Legas, The Cable ta ruwaito.

Ihekweazu ya ce lallai ya yi na'am da shawaran bude makarantu.

Diraktan ya ce Najeriya ta fi kowace kasa yawan adadin yara maras zuwa makaranta a duniya, kuma cigaba da ajiyesu a gida babban illa ne.

Ya ce yanzu haka yara milyan 10 ba sa zuwa makaranta.

"Kun ga dalilin da yasa abubuwan da suka shafi bude makarantu ke yiwa gwamnati wuya; ta yaya zaka daidaita hana yaduwar cutar da kuma wasu abubuwa da yaran ke bukata don cigabansu?" yace.

"Ni dai ina goyon bayan shawaran da gwamnatin tarayya tayi na bude makarantu kuma muyi kokarin rage illolin."

"Idan abubuwa suka munana, kila mu canza shawara amma duka mun fahimci cewa kullen na da illa kan yara."

KU DUBA: Sunday Igboho ya dira Igangan domin fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa

Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC
Amfanin bude makarantu ya rinjayi tsoron kamuwa da Korona, shugaban NCDC
Source: UGC

KU DUBA: Fitittikan Fulani daga kasar Yarbawa: Kama da ni idan ka isa, Igboho ga gwamnan Oyo

A wani labarin kuwa, mai horas da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane, ya kamu da COVID-19 kamar yadda kulob din ya bada sanarwa a ranar Juma’ar nan.

Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa Zinedine Zidane ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.

“Kungiyar kwallon kafan Real Madrid ya na sanar da cewa gwaji ya nuna mai horas da ‘yan wasanmu, Zinedine Zidane, ya kamu da cutar COVID-19.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel