Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje

- Gwamna Ganduje ya yi barazanar kulle kasuwanni idan ba ayi hattara ba

- Ganduje ya yi alhinin waiwayen annobar Korona na biyu inda ta hallaka mutane 17

- Gwamnan ya ce cutar yanzu ta fi tsanani fiye da lokacin bullarta ta farko

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce jihar na shirye-shiryen yiwa mutane gwajin cutar Korona a iyakokin shiga jihar.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin zama da kwamitin yaki da Koronan jihar.

A cewar gwamnan, wadanda ke shirin shiga jihar wajibi ne ayi musu gwajin Korona, domin rage yaduwar cutar a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin ta shirya amfani da sarakunan gargajiya wajen wayar da kan mutane kan hanyoyin kare kansu daga cutar.

"Zamu hada kai da Malamai, makarantu; na gwamnati da masu zaman kansu, jami'o'i, dss. Hakazalika mun ja hankalin kasuwanni. Saboda haka zamu yi amfani da su wajen tabbatar da ana bin dokoki," Ganduje yace.

"Ta haka, muna da tabbaci zamu iya dakile wannan matsalan a jiharmu."

Mataimakin shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jihar, Sabitu Shanono, yace akalla mutane 17 sun mutu a jihar Kano sakamakon cutar tsakanin Disamba 2020 da 19 ga Junairu, 2021.

Ya kara da cewa tun lokacin da cutar ta bulla a jihar a 11 ga Afrilun 2020, mutane 71 sun mutu.

KU KARANTA: Kotu ta jefa direba Kurkuku kan kashe N2m da aka tura masa cikin kuskure

Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje
Za mu fara yiwa duk mai son shiga Kano gwajin Korona, Ganduje Hoto: @NCDCgov
Asali: UGC

KU KARANTA: Ubale Yusufu ya na goyon bayan kujera ta koma yankin Kudu bayan mulkin Buhari

A bangare guda, gwamatin tarayya ta hannun majalisar kolin tattalin arzikin Najeriya watau NEC, ta bada dama a kirkiro magungunan cutar COVID-19 a gida.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 21 ga watan Junairu, 2021, cewa an yi hurumi a fito da magungunan COVID-19 a Najeriya.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kuma bayyana cewa kofa a bude ta ke ga mutanen kasashen waje su shigo da maganin COVID-19 cikin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng