Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon IGP, Gambo Jimeta, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa tsohon IGP, Gambo Jimeta, rasuwa

- Tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya, Alhaji Gambo Jimeta ya rasu

- Kanin marigayin, Abdulrahman Adamu, ya tabbatar da rasuwarsa

- Za a yi jana'izar marigayi Jimeta a birnin tarayya Abuja gobe bayan sallar Juma'a

Tsohon Sifeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Alhaji Gambo Jimeta ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Kanin tsohon shugaban 'yan sandan, Abdulrahman Adamu, ya tabbatar da rasuwarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

Tsohon Sifeta Janar na 'Yan Sanda, Gambo Jimeta ya rasu
Tsohon Sifeta Janar na 'Yan Sanda, Gambo Jimeta ya rasu. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Adamu, tsohon ministan harkokin cikin gida, ya ce za a gudanar da jana'izar Jimeta a ranar Juma'a bayan sallar Juma'a a masallacin kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

KU KARANTA: Wanda na fara sace wa shine tsohon saurayi na da ya ƙi aure na, in ji mai garkuwa, Maryam

An haife marigayin ne a ranar 15 ga watan Afrilun 1937. An nada Jimeta a matsayin sufeta janar na 'yan sanda a shekrar 1986 inda ya maye gurbin Etim Inyang shi kuma daga bisani Aliyu Attah ya gaje shi a shekarar 1990.

Har wa yau, shine mai bada shawara kan harkokin kasa ga tsohon shugaban kasar mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel