Tsadar farashin Siminti: Laifin Korona da #EndSARS ne, gwamnatin tarayya

Tsadar farashin Siminti: Laifin Korona da #EndSARS ne, gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa farashin siminti yayi tashin gwauron zabo

- A makonnin bayan nan, farashin Siminti ya yi tashin da ya ke sa mutane korafi

- A yanzu, farashin Siminti guda daya kan kai N4000 a kasuwa

Gwamnatin tarayya ta ce zanga-zangar #ENDSARS da annobar COVID-19 ne suka haddasa tsadar farashin siminti a Najeriya saboda wadannan abubuwa biyu suka hana kamfanoni ayyukansu.

Sakataren ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Nasir Sani-Gwarzo ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudana a Abuja.

Ya ce Korona da EndSARS sun illata ajiyan Siminti da kuma tsadar kudin tafiyar da Simintocin.

Binciken Vanguard a kasuwanni sun nuna cewa farashin Siminti da abubuwan dake da alaka da shi irinsu bulo, na hauhawa a birnin tarayya , Abuja da sauran jihohin Najeriya.

Misali, farashin kilo 50 na Siminti yanzu ya kai N3,700 a Legas da Cross River; N,4000 a Enugu da Imo; N4,300 a jihar Rivers; sannan N3,500 a Kano da Oyo.

Hakazalika farashin Bulo inci 9 ya tashi zuwa N200, kuma inci 6 zuwa N160 a birnin tarayya.

Gabanin wannan hauhawa, farashin Siminti na tsakanin N2,400 da N2,700.

Jawabi kan haka, Sani-Gwarzo ya gargadi yan Najeriya kada suyi gaggawar sayan Siminti domin boyewa suna tsammani farashin zai kara tashi su samu riba.

Ya ce ma'aikatar na iyakan kokarinta wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda za'a sauko da farashin.

DUBA NAN: Uwargidar Zakzaky, Hajiya Zeenatu, ta kamu da Coronavirus

Tsadar farashin Siminti: Laifin Korona da #EndSARS ne, gwamnatin tarayya
Tsadar farashin Siminti: Laifin Korona da #EndSARS ne, gwamnatin tarayya Hoto: Guardian
Asali: UGC

DUBA NAN: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa masu batanci ga Annabi 2 a Kano

A wani labarin kuwa, gwamnatin tarayya ta ce sahun farko na magungunan cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer suka hada zai shigo Najeriya zuwa karshen Junairun bana.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban hukumar kiwon lafiya na NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib, ya na wannan jawabi a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Faisal Shuaib ya bayyana haka ne yayin da 'yan jarida suka ziyarci wasu dakuna na musamman da aka yi tanadi domin ajiye wadannan magunguna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel