Yanzu-yanzu: Uwargidar Zakzaky, Hajiya Zeenatu, ta kamu da Coronavirus
- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara
- Tun watan Disamban 2015, El-Zakzaky da iyalansa na tsare wajen hukuma
- Kusan makonni biyu a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum
Uwargidar shugaban kungiyar mabiya akidar Shi'a a Najeriya, Hajiya Zeenatu Zakzaky, ta kamu da cutar Coronavirus, an samu labari ranar Alhamis.
'Dan El-Zakzaky, Mohammed, ya tabbatar da halin da mahaifiyarsa ke ciki a jawabin da ya baiwa manema labarai.
Yace: "Kwanaki shida da suka gabata bayan Likitocin iyayena sun kai ziyara gudan tarin Kaduna, mahaifiyata ta fara korafin gajiya, zazzabi da kuma rashin iya shinshinan abu."
"Likitocin suka yi mata gwaje-gwaje domin fahimtar matsalan. Daga ciki akwai na cutar COVID-19."
"Sakamakon gwajin ya nuna ta kamu da cutar COVID-19."
DUBA NAN: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa masu batanci ga Annabi 2 a Kano
DUBA NAN: NPHCDA: Nan da karshen Junairu ake sa ran a kawo magungunan COVID-19
Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce kawo yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya yanzu ya zarce 112,000 cikin samfuri milyan daya da aka gwada.
Mutane 1,301 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Talata, 18 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 113,3015 a Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng