Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa masu batanci ga Annabi 2 a Kano

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa masu batanci ga Annabi 2 a Kano

- Bayan watanni hudu da daukaka karar da Yahaya Sharrif yayi, kotun tayi watsi da hukuncin kotun Shari'a

- Hakazalika kotun ta wanke wani yaron da aka yankewa hukuncin shekara 10 a Kurkuku

- Alkali Nuradden Sagir, shine wanda ya yanke hukuncin ranar Alhamis

Kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Kano ta yi watsi da hukuncin daurin shekaru 10 da akayi wa Umar Farouq, matashin da ake zargi da kalaman batanci ga Annabi.

Bayan haka, kotun ta sake watsi da hukuncin da aka yiwa mawaki, Yahaya Aminu Sharif, inda ta ce a sake shari'ar daga farko, cewar rahoton BBC.

Shi ma Yahaya Aminu Sharrif ana zarginsa da kalaman batanci kan Annabi (SAW).

Alkali Nuradden Sagir, shine wanda ya yanke hukuncin ranar Alhamis.

Ya ce hukuncin da aka yanke a farko na cike da kura-kurai kuma ko lauya ba'a bashi ba.

A cewarsa, hukuncin da kotun Shari'ar tayi ya sabawa Sashe 2-6-9 na ACJ.

DUBA NAN: Uwargidar Zakzaky, Hajiya Zeenatu, ta kamu da Coronavirus

KU KARANTA: Mawakin da yayi batanci ga Annabi ya daukaka kara

Watanni hudu da suka gabata mun kawo muku cewa lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama dake zaune a jihar Kano sun bayyana tsoronsu kan taimakawa Yahaya Sharrif-Aminu, mawakin da yayi batanci ga manzon Allah (SAW).

Wannan shine dalilin da yasa har yanzu ya gaza daukaka karar hukuncin kisan da kotun shari'ar ta yanke masa ranar 10 ga Agusta, 2020.

Yahaya Sharif-Aminu na da wa'adin kwanaki 30 da zai iya daukaka kara kafin a iya zartar da hukuncin da kotu ta yanke kansa kuma yanzu saura kwanaki goma wa'adin ya kare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel