NPHCDA: Nan da karshen Junairu ake sa ran a kawo magungunan COVID-19

NPHCDA: Nan da karshen Junairu ake sa ran a kawo magungunan COVID-19

- Gwamnatin Tarayya ta ce a karshen Junairu za a aiko magungunan COVID-19

- Shugaban NPHCDA na kasa, ya shaidawa ‘Yan jarida wannan cikin makon nan

- Faisal Shuaib yace za a raba wa manyan kasa da ma’aikatan lafiya magungunan

Gwamnatin tarayya ta ce sahun farko na magungunan cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer suka hada zai shigo Najeriya zuwa karshen Junairun bana.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban hukumar kiwon lafiya na NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib, ya na wannan jawabi a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Faisal Shuaib ya bayyana haka ne yayin da 'yan jarida suka ziyarci wasu dakuna na musamman da aka yi tanadi domin ajiye wadannan magunguna.

A cewar Dr. Faisal Shuaib, za a aiko wa Najeriya kwayoyi 100, 000 ne na wannan sabon maganin.

KU KARANTA: Ana damfarar mutane da sunan COVID-19 a Abuja

A jawabin na sa, shugaban hukumar NPHCDA bai fadi ainihin ranar da za a kawo maganin ba, amma ya tabbatar da cewa zuwa karshen watan nan za su shigo.

Dr. Shuaib yake cewa gwamnatin tarayya za ta maimaita irin kokarin da ta yi wajen yakar cutar Polio domin ganin an ci karfin annobar Coronavirus a kasar nan.

Za a yi amfani da magungunan ne a kan mutanen Najeriya 50, 000. Za a fi bada muhimmanci a kan ma’aikatan lafiya da su ke hadu wa da masu dauke da cutar.

Haka zalika za a ba mala’u daga cikin al’umma, musamman gwamnonin jihohi, sarakunan da sauran masu sarautar gargajiya da kuma malaman addini maganin.

KU KARANTA: Kashe N400bn kan maganin COVID-19 asara ce - Attahiru Bafarawa

NPHCDA: Nan da karshen Junairu ake sa ran a kawo magungunan COVID-19
Maganin COVID-19 Hoto: dailytrust.com
Asali: Getty Images

Kowane mutum zai samu kwayoyi biyu, amma kafin nan sai hukumar NAFDAC ta tabbatar da ingancin maganin, don haka ya ce jama’a su kwantar da hankalinsu.

Bugu da kari, ana tsammannin za a fara hada irin wannan magani a Najeriya nan da watan gobe.

Duk wannan abu da ake yi, gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya fito fili ya nuna cewa ba ya na'am da mutane su yi amfani da wannan magani da ake magana.

Tuni kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF ta yi martani ga ikirarin da gwamna Yahaya Bello ya ke yi mara tushe a game da rigakafin wannan cuta ta COVID-19.

Daraktan kungiyar, Ashishana Okauru, ya fada wa 'yan jarida cewa gwamnoni na duba yiwuwar amfani da dabarun wayar da kan al'umma a kan aiki da magungunan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel