Yin rowa ga fastonka zai iya sa ka yi mutuwar kuruciya, Fasto ya ja kunnen SMAN

Yin rowa ga fastonka zai iya sa ka yi mutuwar kuruciya, Fasto ya ja kunnen SMAN

- Wani faston Najeriya mai suna Goodheart Val Aloysius ya ja kunnen kungiyar samari marowata na kasar nan

- Ya ce kada su kuskura rowar su ta taba fastoci da kuma majami'u saboda hakan ba zai zama abu mai kyau garesu ba

- Kamar yadda ya wallafa a Facebook, ya ce babu shakka za su yi mutuwar kuruciya matukar suka fara rowa ga fastoci

Wani faston Najeriya mai suna Goodheart Val Aloysius ya ja kunnen maza 'yan kungiyar Samari Marowata na Najeriya.

Ya gargadesu da kada su kasance masu nuna halayyar rowarsu ga fastocinsu.

Kamar yadda fasto Aloysius yace, yin halyayyar rowa ga fastonka zai iya sa ka mutu kana da kuruciya.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke jami'in tsaron ABU da ke taimakawa masu garkuwa da mutane

Yin rowa ga fastonka zai iya sa ka yi mutuwar kuruciya, Fasto ya ja kunnen SMAN
Yin rowa ga fastonka zai iya sa ka yi mutuwar kuruciya, Fasto ya ja kunnen SMAN. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

Faston ya wallafa wannan jan kunnen ga samarin marowata a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda ya wallafa: "Ina fatan wannan kungiyar ta samari marowata ba za ta taba fastoci ba da majami'u. Saboda rowa ga fastoci za ta iya sa mutum yayi mutuwar kuruciya. A kiyaye."

KU KARANTA: Bauchi: An daurawa matashi aure da gawar budurwarsa a kan sadaki N2000

A wani labari na daban, mutane akalla 10 ne suka rasa rayukansu da gidajensu bayan 'yan bindiga sun kai wa 'yan kauyen Talli, Dutsin Gari da Rayau dake karamar hukumar Maru a jihar Zamfara farmaki, kamar yadda Daily trust ta ruwaito.

Mazauna garin sun sanar da manema labarai cewa wasu 'yan bindiga sun je Dutsen Gari a baburansu da niyyar su yi garkuwa da mazauna garin, ba su san 'yan kauyen suna da cikakken shirinsu ba.

Take a nan aka fara musayar wuta tsakanin 'yan bindigan da 'yan kauyen wanda aka yi sa'o'i da dama ana yi. Bayan ganin ba za su samu nasara ba 'yan bindigan suka tsere daga kauyen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel