'Yan sanda sun cafke jami'in tsaron ABU da ke taimakawa masu garkuwa da mutane

'Yan sanda sun cafke jami'in tsaron ABU da ke taimakawa masu garkuwa da mutane

- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da damke wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane

- An gano cewa suna daga cikin masu garkuwa da mutane da suka addabi jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

- 'Yan sandan sun kara da damke wani jami'in tsaro na jami'ar da ke taimakawa masu garkuwa da mutanen

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta damke wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Daily Trust ta wallafa.

An kama daya daga cikin ma'aikatan tsaro na jami'ar mai suna Aliyu Abubakar sakamakon bai wa masu garkuwa da mutanen tallafi a dukkan lokutan da suke sace jama'a a jami'ar.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, CP Frank Mba, ya sanar da damke wani Malam Jafaru da ke samar da asiri ga masu garkuwa da mutanen.

KU KARANTA: Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

'Yan sanda sun cafke jami'in tsaron ABU da ke taimakawa masu garkuwa da mutane
'Yan sanda sun cafke jami'in tsaron ABU da ke taimakawa masu garkuwa da mutane. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Tun a karshen shekarar da ta gabata ne masu garkuwa da mutane suka dinga sace farfesoshi da ke zama a cikin rukunin gidajen malaman jami'ar.

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya harbi farar hula 4

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata matar aure mai shekaru 20 mai suna Suwaiba Shuaibu a kan zarginta da sokawa wata Aisha Kabir wuka ana sauran kwanaki kadan aurenta.

An gano cewa Aisha ce wacce Malam Shahrehu Alhaji Ali, mijin wacce ake zargin zai aura a ranar 9 ga watan Janairu a kauyen Gimawa, karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce an nema amaryar an rasa amma daga baya sai aka ga gawarta a wani kango.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel