Bauchi: An daurawa matashi aure da gawar budurwarsa a kan sadaki N2000

Bauchi: An daurawa matashi aure da gawar budurwarsa a kan sadaki N2000

- Wani matashi ya biya sadakin gawar budurwarsa N2000 inda aka daura musu aure kafin jana'iza

- An gano cewa Salisu da Halima masoyan juna ne na hakika wadanda suka dauka alkawarin aure

- Bayan mutuwarta ne mahaifiyarta ta sanar da wasiyyarta na cewa a daura mata aure da Salisu ko babu ranta

Wani matashi mai suna Mohammed Salisu da ke yankin Abujan Kwata a jihar Bauchi a makon da ya gabata ya aura matacciyar budurwarsa mai suna Halima.

An daura auren kuma har ya biya sadaki N2000 ga 'yan uwan Halima.

Jaridar Blueprint ta gano cewa, mamaciyar ta bar wasiyyar cewa ko ta rasu 'yan uwanta su aura mata Salisu.

KU KARANTA: Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

Bauchi: An daurawa matashi aure da gawar budurwarsa a kan sadaki N2000
Bauchi: An daurawa matashi aure da gawar budurwarsa a kan sadaki N2000. Hoto daga Blueprint.ng
Source: UGC

An gano cewa Salisu da Halima sun dade suna soyayya kuma su biyun sun tabbatar da cewa za su rikewa juna amana.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Malam Banhajatu Nasir na hukumar Shari'ah na jihar Bauchi, ya yi bayanin cewa an daura auren ne lokacin da mahaifiyar marigayiyar ta bayyana wasiyyar diyarta yayin da ake shirin jana'iza.

Ya ce limamin da ya daura auren tare da wanda ya karbawa angon auren duk sun shiga hannun hukumarsu.

A yayin tsokaci a kan wannan cigaban, babban malami kuma babban limamin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Sheikh Dr Mansur Yelwa ya kushe wannan auren inda yace tamkar babu ne.

KU KARANTA: Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar

A wwani labari na daban, mutanen Maiduguri, babban birnin Borno, sun shiga tararrabi bayan an kona wani soja saboda ya harbi fararen hula 4.

Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun sanar da Premium Times yadda wani Mohammed Abdullahi, soja mai lamba 16NA/75/4272 ya harbi wasu fararen hula 4 a ranar Asabar bayan wata hayaniya ta hada su a titin Baga dake kusa da kasuwar garin.

Daya daga cikin fararen hular ya mutu take a wurin yayin da sauran 3 suka samu munanan raunika. Yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel