Bidiyo: Uwargida ta isa wurin da mijinta ke 'auren sirri', ta hargitsa taron

Bidiyo: Uwargida ta isa wurin da mijinta ke 'auren sirri', ta hargitsa taron

- An gwangaje da gagarumar rigima a wurin liyafar wani biki a jihar Abia

- Kamar yadda bidiyon ya bayyana, uwargida tana hargitsa taron bikin mijinta da wata

- Ta sanar da cewa tana da yara hudu da shi amma ya ci amanarta yana auren wata

Wani bidiyo na cin amana karara da ke ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya janyo cece-kuce daga wurin wadanda suka kalle shi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, ta ce bidiyo ne wanda aka dauka yayin da wata matar aure ta isa wurin liyafar auren mijinta da wata mata wacce suka yi auren sirri.

A bidiyon an ga matar rike da hotunan aurenta da mijinta tana bayani inda take cewa cin amanarta kawai za a yi amma mijinta ne yake auren sirri da wata matar.

Bidiyo: Uwargida ta isa wurin da mijinta ke 'auren sirri', ta hargitsa taron
Bidiyo: Uwargida ta isa wurin da mijinta ke 'auren sirri', ta hargitsa taron. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

KU KARANTA: Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

Matar ta fara bayyana a kofar shiga wurin liyafar dauke da hotuna inda take bayyanawa jama'a cewa wannan angon mijinta ne.

Ta kara da sanar da cewa yaransu hudu, maza uku da mace daya. Amma kwatsam sai ta ji labarin aurensa da wata mata.

KU KARANTA: Gumurzun 'yan bindiga da Zamfarawa: Mutum 10 sun mutu, an kone gidaje masu yawa

A wani labari na daban, mutanen Maiduguri, babban birnin Borno, sun shiga tararrabi bayan an kona wani soja saboda ya harbi fararen hula 4.

Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun sanar da Premium Times yadda wani Mohammed Abdullahi, soja mai lamba 16NA/75/4272 ya harbi wasu fararen hula 4 a ranar Asabar bayan wata hayaniya ta hada su a titin Baga dake kusa da kasuwar garin.

Daya daga cikin fararen hular ya mutu take a wurin yayin da sauran 3 suka samu munanan raunika. Yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel