Kano Ta Samu Sauƙi, Ƴan Sanda Sun Yi Ram da Hatsabibin Ɗan Daba

Kano Ta Samu Sauƙi, Ƴan Sanda Sun Yi Ram da Hatsabibin Ɗan Daba

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta kama wani fitaccen dan daba mai suna Sankolo, mai shekaru 22, bisa zargin hannu a satar wani yaro mai shekaru tara
  • An kama Abubakar Isma’il ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2026, bayan samun bayanan sirri sakamakon cafke wani dan daba da ake kira Ta’ambo
  • ’Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya amsa hannu a wasu ayyukan daba da fashi da makami, yayin da ake kokarin cafke sauran mambobin kungiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wani fitaccen dan daba da ake kira Sankolo, bisa zargin hannu a satar wani yaro mai shekaru tara a unguwar Rimin Kebe da ke Kano.

Wanda ake zargin, mai suna Abubakar Isma’il, mai shekaru 22, an kama shi ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2026, da misalin karfe 9:30 na dare.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya nufi fadar White House zai kashe shugaban ƙasar Amurka

Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook.

Kiyawa bayyana cewa kama Sankolo ya biyo bayan bayanan sirri da aka tattara bayan cafke wani da ake zargi da daba, Umar Usman, wanda aka fi sani da Ta’ambo, a ranar 5 ga Nuwamba.

Jami’an rundunar ’yan sanda ta Zango ne suka cafke shi karkashin aikin Operation Kukan Kura.

An zargi Sankolo da satar yaro mai shekaru 9

Kiyawa ya ce Sankolo na cikin jerin mutanen da rundunar ke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata daba da sauran laifuka a Rimin Kebe da yankunan da ke makwabtaka da ita.

Ya kara da cewa ana zargin matashin da hannu a satar Ubaidu Sammani, dan Alhaji Sammani mai shekaru tara, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 3 ga Yuli, 2026.

A cewarsa, tuni aka gurfanar da wasu da ake zargi da hannu a lamarin a gaban kotu, inda ake ci gaba da shari’arsu.

Wanda ake zargin ya amsa laifuffuka

Kara karanta wannan

Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano

Kakakin rundunar ya ce a yayin binciken farko, wanda ake zargin ya amsa hannu a wasu ayyukan daba da fashin wayoyin hannu.

Ya bayyana cewa ana zargin Sankolo da jagorantar hare-hare, tsoratar da mazauna yankin da kwace musu kayayyaki masu daraja.

Ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, yayin da ake kokarin cafke sauran mambobin kungiyar da kuma kwato kayayyakin sata da makaman da ake zargin sun yi amfani da su.

Rundunar ta bayyana cewa za ta gurfanar da shi a kotu bayan kammala bincike domin girbar abin da ya shuka.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaki da laifuffuka.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.