Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya harbi farar hula 4

Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya harbi farar hula 4

- Mutanen Maiduguri sun shiga tararrabi bayan wata hayaniya ta hada wasu fararen hula da wani soja har ya harbi mutane 4

- Daya daga cikinsu ya mutu take a wurin, yayin da sauran 3 suke cikin mummunan yanayi a asibiti, duk da dai an ce ya yi shaye-shaye ne lokacin

- Bayan nan ne matasa suka hassala suka banka wa sojan wuta, sakamakon faruwar hakan kowa yake tsoron sojoji su koma daukar fansa

Mutanen Maiduguri, babban birnin Borno, sun shiga tararrabi bayan an kona wani soja saboda ya harbi fararen hula 4.

Wadanda suka ga yadda lamarin ya faru sun sanar da Premium Times yadda wani Mohammed Abdullahi, soja mai lamba 16NA/75/4272 ya harbi wasu fararen hula 4 a ranar Asabar bayan wata hayaniya ta hada su a titin Baga dake kusa da kasuwar garin.

Daya daga cikin fararen hular ya mutu take a wurin yayin da sauran 3 suka samu munanan raunika. Yanzu haka suna asibiti ana kulawa da lafiyarsu.

KU KARANTA: Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar

Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya kashe farar hula 4
Hankula sun tashi a Maiduguri bayan an babbaka sojan da ya kashe farar hula 4. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

A lokacin da al'amarin ya faru, Abdullahi a bige yake don ya yi shaye-shaye. Bayan faruwar lamarin ne wasu matasa fararen hula suka banka masa wuta a wurin, kamar yadda majiyoyi da dama suka sanar da Premium Times.

Sojan dan bataliya ta 130 ne, amma an hada shi da 'yan bataliya ta 212 na Operation Lafiya Dole sakamakon ta'addanci dake garin.

Wannan lamarin ya yi matukar tayar wa da mutanen dake wuraren Barka Da Zuwa hankali don tsoron kada sojoji su je daukar wa dan uwansu da aka babbaka fansa.

Fararen hula da dama sun tsere daga garin saboda matukar tsoro.

Yayin da jama'a suka cigaba da shiga halin tsoro don gudun a fara karya doka, sai aka tura sojojin Division 7 don su kula da anguwar. Za a cigaba da kulawa da wurin na wani lokaci.

KU KARANTA: An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki

A wani labari na daban, wani dan sanda mai mukamin sifeta ya rasu inda wasu suka raunata bayan harin da 'yan bindiga suka kai jihar Ribas, Channels Tv ta wallafa.

Hukumar 'yan sandan jihar Ribas ta ce kusan 'yan bindiga 17 ne suka kai gagagrumin hari kan jami'an 'yan sandan da aka tura Borikiri a Fatakwal a daren Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni a wata takarda da ya fitar, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Joseph Mukan ya bada umarnin zakulo wadanda suka aikata wannan laifin da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng