Hisbah ta cafke mata 19 a Kano da laifukan baɗala

Hisbah ta cafke mata 19 a Kano da laifukan baɗala

- Hukumar Hisbah ta cafke mata 19 a Kano bisa laifukan badala a jihar

- Hukumar ta ce 18 daga cikin masu laifin basu taba aikata laifin ba kuma ta gargade su

- Hukumar ta ce Kamen na zuwa ne biyo bayan umarnin gwamnati na rufe wuraren shakatawa da gidajen kallo a jihar

Babban kwamandan Hisba na Jihar Kano, Dakta Haruna Ibn Sina, ya ce hukumar ta kama mata 19 a jihar da laifukan badala daban daban a kwaryar birnin Kano, The Punch ta ruwaito.

Kwamandan ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da Malam Lawal Ibrahim, kakakin hukumar ya fitar a ranar Laraba.

Hisbah ta cafke mata 19 a Kano da laifukan baɗala
Hisbah ta cafke mata 19 a Kano da laifukan baɗala. Hoto @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

Ya ce an kama matan ranar 19 ga Janairu, da misalin karfe 9:00 na dare a Nasarawa Park lokacin da suke shan kayan maye a titin Ahmadu Bello.

Ya ce sunyi kamen ne biyo bayan umarnin gwamnatin jihar na rufe gidajen kallo da wuraren taro don kauracewa yaduwar COVID-19 a jihar.

"Duk wanda aka kama mata ne kuma sun haura shekara 20.

"18 daga ciki ba a taba kama su ba, daya kuma an taba kama ta," a cewar sa.

KU KARANTA: FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa

Ya shawarci iyaye da su daina siyawa yayan su manyan wayoyi, su kuma basu tarbiya mai kyau.

A wani rahoto an mika wanda aka kama a karon farko ga iyalan su tare da gargadi, dayar kuma za a bata kulawa ta musamman.

Kamfanin dillancin na kasa (NAN) ta ruwaito an haramta ayyukan badala a karkashin shari'ar musulunci a Jihar Kano.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel