'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

- Tiffany Trump ta sanar da baikon ta da saurayin ta mai alaka da Najeriya

- Yar shugaban na Amurka mai barin gado ta sanar da baikon ta da Michael wanda ya tashi a Lagos a shafin ta na Instagram

- Ta bayyana baikon ta da Michael a matsayin babban abun farin ciki kafin barin su fadar White House

Tiffany Trump, yar shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump, a ranar Talata, ta sanar da baikon ta da saurayin ta, Michael Boulos, The Punch ta ruwaito.

Yar mai shekaru 27, ta sanar da labarin a shafin ta na Instagram, awanni kadan kafin wa'adin mulkin mahaifin ta.

'Yar shugaban Amurka Trump zata auri saurayinta da ya girma a Nigeria
'Yar shugaban Amurka Trump zata auri saurayinta da ya girma a Nigeria. Hoto:@MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo da Hotuna: Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto

Iyalan za su bar White house safiyar Laraba yan awanni kafin rantsar da Joe Biden na jam'iyyar Democrat a matsayin shugaban Amurka na 46.

'Yar shugaban Amurka Trump zata auri saurayinta da ya girma a Nigeria
'Yar shugaban Amurka Trump zata auri saurayinta da ya girma a Nigeria. Hoto: Chip Somodevilla/Getty Images
Asali: Getty Images

"Abin farin ciki ne mun cimma abubuwa da dama, ababen tarihin da iyalai na a nan fadar White House, ba abin da yafi kamar baiko na da Michael! Ina farin ciki da alfaharin fara sabuwar rayuwa!" inji Tiffany.

Tiffany da Michael mai shekara 23 sun fara soyayya tun 2018.

A rahoton Wikipedia, Michael, dan asalin tsatson Faransa da Lebanon, ya girma a Lagos, Najeriya.

Baban Michael, Massad, shine shugaban SCOA a Najeriya sannan mahaifiyar sa, Sarah, ita ce ta samar da Society for the Performing Arts a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

Iyalan sun dawo Lagos inda harkokin kasuwancin su ya ke lokacin Michael ya na karami.

A Najeriya, Michael ya kammala makarantar American International School a Lagos. Sai ya koma London, inda ya samu digirinsa na farko a fannin Global Business Management daga jami'ar Regent London a 2018, sai digirinsa na biyu a fannin Project Management, Finance and Risk a jami'ar Landon a 2019.

Shi ne mataimakin daraktan SCOA a Najeriya tun 2016, daraktan Fadoul Group tun 2019, kuma shugaban ci gaban kasuwancin kamfanin Royalton Investment tun 2019.

Ana tsammanin buga gangar auren masoyan kwana nan.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel