FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa

FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa

- Gwamnatin tarayya ta yi tir da korar makiyaya da gwamnan jihar Ondo ya yi daga jiharsa

- Gwamnatin ta ce suma yan kasa ne kuma ya kamata a kare kamar kowa

- A jiya Litinin ne Akeredolu ya bawa makiyaya da ke dajikan jihar wa'adin mako guda su fice daga cikin su

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soki umarnin gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na korar makiya daga dazukan Jihar Ondo.

Premium Times ta ruwaito umarnin Akeredolu a ranar Litinin, a wani mataki na dakile garkuwa da mutane a jihar.

FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa
FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa. Hoto: @NGRPresidency
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Trump ta kafa wani tarihi kwanaki biyu kafin sauka daga mulki

"Cikin kwana 7, makiyaya su bar dazukan jihar nan, daga yau zuwa Litinin 18 ga Janairun 2021," a cewar gwamnan.

A martanin ta ranar Talata, fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Mr Akeredolu, babban lauya, "ba za a tsammaci ya kori dubban makiyan da rayuwar su ta dogara da jihar ba bisa yan ta'addan da suka mamaye daji ba.

"Gwamnatin Ondo, da sauran 35 na kasar nan dole ne su dinga bambance yan ta'adda da kuma yan kasa masu bin doka wanda suma dole ne a kare rayukan su. Karkashin doka da oda, yaki da ta'addanci yaki ne na ceto kimar dan Adam wanda ya rataya a hannun kasar mu."

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana bukatar da ke akwai na rashin danganta yanki, kabila ko addini da laifuka ko ta'addanci sai dai a ware laifin gefe guda a magance shi.

KU KARANTA: Bidiyo da Hotuna: Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto

Gwamnatin ta ce bata yi tsamanin mutum kamar Akeredolu wadda babban lauya ne mai mukamin SAN zai dauki mataki irin wannan da sunan korar bata gari.

Wani sashi na sakon ya ce, "Muna son fayyace cewa garkuwa da mutane, fashi da satar shanu dukkansu laifi ne ko da wanene ya aikata. Amma, danganta laifi da wasu yankuna, harshe, ko addini kamar yadda wasu ke yi kan kuskure zalunci ne."

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel