Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar PDP rasuwa

Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar PDP rasuwa

- Cif Linus Okom, jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya riga mu gidan gaskiya

- Marigayin ya rasu a gidansa da ke Calabar babban birnin Cross Rivers a ranar Talata 19 ga watan Janairu

- Mamba mai wakiltar Bekwara a majalisar dokoki, Edward Ajang ya tabbatar da rasuwarsa inda ya ce babban rashi ne ga kasa baki daya

Jigo a jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Cross Rivers, Cif Linus Okom ya rasu a ranar Talata, Vanguard ta ruwaito.

Cif Okom wanda aka fi sani da Ada Bekwara ya rasu ne a gidansa da ke Calabar, Jihar Cross Rivers babban birnin jihar bayan gajeruwar rashin lafiya.

DUBA WANNAN: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar PDP rasuwa
Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar PDP rasuwa. Hoto: @vanguardngrnews
Source: Twitter

Ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. An haife shi ne a shekarar 1940 ya kuma shiga aiki na rundunar yan sandan Najeriya bayan ya yi murabus ya shiga siyasa a jamhuriya ta biyu sannan an nada shi kwamishinan noma a 1983.

Shine shugaban jam'iyyar All Peoples Party, APP, a 1988 sannan ya koma PDP a shekarar 2000 inda ya zama jagoran PDP na mazabar arewacin jiharsa.

Da ya ke tabbatar da rasuwarsa, Mista Edward Ajang, mamba mai wakiltar Bekwara a Majalisar Dokoki ya ce rasuwar Cif Okom babban rashi ne ga jihar da kasa baki daya.

KU KARANTA: FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa

"Mutum ne mai taimakon gajiyayyu kuma da wuya wani ya tafi neman taimako wurinsa ya dawo da bacin rai duk halin da ya ke ciki.

"Katanga ta fadi kuma za a yi wahalar samun wanda zai maye gurbin da ya bari na tsawon lokaci."

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel