Budurwa ta yi ƙarar fasto saboda raba ta da kadarorinta da sunan zai aure ta

Budurwa ta yi ƙarar fasto saboda raba ta da kadarorinta da sunan zai aure ta

- Budurwa tayi karar malamin addini bayan ya ƙi cika alkawarin aurenta da ya dauka

- Budurwar ta shaidawa kotu cewa ya raba ta da duk abin da ta mallaka kafin ya yaudareta

- Da aka karanta masa tuhumar ya karyata kuma an gan shi da wata budurwar da aka ruwaito anyi musu baiko

Wata budurwa, Kwanye, ta yi karar wani fastor mai shekaru 28, Marwa Tumba, tare da shaidawa Mai shari'a Nuhu Musa Garta cewa, Marwa ya yi alkawarin auren ta sai dai ya yaudare ta ya koma wurin wata bayan ya cinye mata kudade ya bata mata rayuwa.

Ta shaidawa kotu cewa ta fara haduwa da shi ne a wajen taron addu'a a Yolde Pate, a karamar hukumar Yola South a 2019, in da ya shaida mata cewa ya gano mata mijin aure, The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

Budurwa ta yi karar fasto da ta ce ya yaudare ta da aure
Budurwa ta yi karar fasto da ta ce ya yaudare ta da aure. Hoto: @MobilePunch
Source: UGC

A cewar ta, Fasto Marwa ya shaida mata cewa yanzu ita matarsa ce kuma ya ce ta fara "bada sadaka".

Tace ta fara bada sadakar naira dubu daya kamar yadda ya bukata.

Tace daga ya fara kai mata ziyara gidan ta a lokacin tana aiki da kungiyoyin sa kai, inda ya yi alkawarin shi zai aure ta kamar yadda ya gano.

Kuma daga bisani ya saka ta ajiye aiki tare da siyar da gidan nata kafin su yi aure, kuma ta yarda ta mika takardar ajiye aiki ta kuma siyar da gidan ₦500,000.

Ta ce lokacin da aka biya kudin gidan ta tura masa la'ada ta ₦50,000 kuma tayi amfani da sauran kudin wajen yi wa coci hidima lokaci zuwa lokaci har kudin suka kare.

Ta ce har akwai lokacin da ya bukaci ta bashi jerin abin da ake bukata a aure, kuma ta ba shi.

DUBA WANNAN: FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa

Ta ce ya tura ta Michika wajen iyayen ta, inda ya ce zai zo daga baya don a daddale magana amma bayan shafe kwanaki bata gan shi ba, iyayen ta suka kore ta bayan sun gano mayaudari ne.

Ta ce ya daina kiranta, kuma bayan ta dawo Yola ta nemi inda yake ta rasa.

Ta shaida cewa ya wulakantar da ita bayan ya cinye mata kudade, ya sa ta ajiye aiki, ta siyar da gidanta ta kuma zama abar tausayi, ta ce yanzu tana zaune a wani kango inda ta ke siyar da kayan miya.

Da aka karanta masa tuhumar faston ya karyata.

Daga nan, lauyan shi, M. A Mohammed ya roki kotu da ta bada belin wanda ya ke karewa, kuma kotun ta bayar tare da dage sauraren karar zuwa 4 ga Fabarairu don bawa mai kara damar gabatar da shaidu.

A zaman kotun na ranar Talata, anga Pastor Marwa da wata budurwar, wanda jaridar Punch ta ruwaito anyi musu baiko.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel