Kotu ta bayar da umarnin a lika takardar sammaci a ofishin Dogara

Kotu ta bayar da umarnin a lika takardar sammaci a ofishin Dogara

- Wata kungiya mai lakabin UGPRO ta sake shigar da karar Yakubu Dogara a gaban kotun tarayya da ke Abuja

- A ranar Litinin ne kotun ta saurari karar da jam'iyyar PDP ta shigar da Dogara tare da bayyana cewa ba mambanta bane

- Dukkan masu karar na neman kotun ta tsige Dogara saboda ya samu nasara ne a karkashin inuwar jam'iyyarsu

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a like takardar sammacin karar da PDP ta shigar a ofishin Yakubu Dogara da ke majalisar wakilai.

A ranar Talata ne alkalin kotun, Okon Abang, ya saka ranar 5 ga watan Fabarairu domin bayyanar Dogara a gabansa.

Sai dai, masu kara; kungiyar UGRPO, sun yi zargin cewa Dogara ya dakile duk wani yunkuri na damka masa sammacin kotu.

Duk da lauyan Dogara ya garzaya zuwa kotu wurin Jastis Abang domin karbar sammacin, Alkalin ya ce zai fi kyautuwa a lika takardar a ofishin Dogara.

Kungiyar UGRPO, a ranar Talata, ta shigar da sabuwar karar neman kotu ta tsige Dogara bayan wacce jam'iyyar PDP ta shigar, kamar yadd Premiumtimes ta rawaito.

A dukkanin karar, masu kara sun roki kotu ta tsige Dogara saboda ya sauya sheka zuwa APC bayan samun nasararsa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

KARANTA: Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Teti, shekara fiye da 2,500 baya

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan PDP, Mista Jubril, ya roki kotu ta daga kafa wajen sauraron karar saboda har yanzu Dogara yana sharbar romon zaman mamba a majalisa da tikitin jam'iyyarsu.

PDP: Kotu ta bayar da umarnin a lika takardar sammaci a ofishin Dogara
PDP: Kotu ta bayar da umarnin a lika takardar sammaci a ofishin Dogara
Asali: Twitter

Masu Kara; PDP da shugabanta na jihar Bauchi, Hamza Koshe Akuyam, sun bukaci Dogara ya bar kujerarsa bisa dogaro da sashe na 68(1) na kundin tsarin mulki, kamar yadda Channels ta rawaito.

A cewarsa, doka ta bukaci dan majalisa ya sauka daga kujerarsa matukar ya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar daban ba tare da jam'iyyarsa na fuskantar wani rikici ba.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

A cewarsu, bai kamata ko kadan Dogara ya cigaba da zama a zauren majalisa da nasarar da ya samu da sunan PDP ba.

A wai labarin daban, Legit.ng ta rawaito cewa wasu 'yan bindiga sun kashe wata dattijuwa, Hauwa Umaru, mai shekaru 80 a kauyen Sharu a karamar hukumar Igabi a jihar kaduna.

Kazalika, 'yan bindigar sun kashe jami'an 'yan sanda hudu yayin musayar wuta a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.

Duk da hakan, IGP Mohammed Adamu ya jinjinawa tawagar 'yan sanda saboda ta dakile harin da 'yan bindigar suka kai musu yayin da suke kan hayarsu ta komawa Kano bayan kammala wani aiki na musamman.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel