Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya

Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya

- Masu tonon ma'adanan karkashin kasa (Archaeologists) sun tono wasu muhimman kayan masu dumbin tarihi

- Sun tono kayan ne bayan sun gano wata makabarta da aka gina a karkashin kasa a Saqqara da ke kudancin Cairo

- An samu matattun mutane da makamansu, wasu kuma da litattafai, a cikin akwatin saka gawa

A ranar Asabar ne kasar Misra, wacce yanzu ake kira 'Egypt', ta sanar da cewa wasu masu binciken ma'adanan karkashin kasa sun bankado wani tsohon tarihi a Saqqara da ke kudancin Cairo.

Masu binciken sun gano wata makabarta a karkashin kasa wacce fitaccen masanin tarihin Egypt, Zahi Hawass, ya ce an ginata ne a matsayin wurin binne Sarauniya Naert, kamar yadda Channels ta rawaito.

Sarauniya Naert mata ce wurin Fir'auna Teti, Sarki na farko a gidan masarauta ta 6 da ta mulki kasar Misra.

Ita kanta makabarta an gano ta ne daura da ginin tsibirin da aka binne shi kansa Fir'auna Teti a karni na 11 kafin zuwan Annabi Isa (BC).

A cewar Hawass, gano makabartar zai cike wani gurbin tarihi da aka dade ana nema domin fahimtar alakar tsakanin wasu al'amura na karni 16 da na karni 11 kafin zuwan Annabi Isa.

Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya
Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya @Channeltv
Asali: Twitter

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya
Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Tieta, shekara 2,500 baya @Thenation
Asali: Twitter

An gano wasu akwatunan katako da kuma wasu kaya da kaya da aka sassaka da itace wanda binciken kimiyya ya gano cewa an kera su fiye da shekaru 2,500 da suka gabata.

KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya rasu ya bar Rolls Roys 10

A cikin akwatinan, wadanda aka binne a ramuka fiye da hamsin, akwai gawa dauke da wasu kaya da suka hada da litattafai da makaman yaki.

Sauran kayan da aka samu sun hada da fuskoki da aka sassaka daga itace, kwale-kwale da takaitaccen rubutu a jikinsa da aka tsakuro daga wani littafi da aka bayyana da 'littafin mutuwa'.

Kayayyakin sun nuna alamar cewa gawarwakin sojoji ne irin na tsohuwar masarautar Misra mai dumbin tarihi.

A kwanakin baya ne ministan gargajiya da bunkasa harkokin bude ido a kasar Egypt, Khaled al-Anani, ya sanar da cewa da sauran abubuwan tarihi da za'a iya cigaba da ganowa a Saqqara.

Legit.ng ta taba wallafa cewa Gidan adana kayan tarihi na Turkiyya ya wallafa hotunan wasu kayayyakin da annabi ya yi amfani da su.

Akwai ɗumbin kayan tarihi da ake samu a Santambul da ba kasafai ake samunsu daga sauran sassan duniyar da Musulunci ya mulka a baya ba.

Shahararren malamin addinin Islama a arewacin Nigeria, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyanawa gidan labarai na BBC dalilin da yasa ake jingina Annabi da kayan tarihi da aka samu a Turkiyya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng