An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano

An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano

- Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano sun kai samame tare da cafke wasu mutane hudu da ake zargi da garkuwa da mutane

- Daga cikin mutanen hudu har da wata mace da ak kashe mijinta a cikin 'yan bindiga a jihar Zamfara

- Matar ta shiga sana'ar garkuwa da mutane bayan an kashe mijinta, a cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ta kai samame gidan wasu batagari da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Kano.

A cewar rundunar, jami'anta sun samu nasarar cafke mutane hudu gidan, cikinsu har da wata mace.

Da yake tabbatar da hakan ga jaridar TheCable, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, ya ce an kama mutanen yayin samamen da jami'an tsaro suka kai gidan da ke kauye Jaba, karamar hukumar Ungogo.

A cewar kakakin, binciken rundunar 'yan sanda ya gano cewa matar da aka kama ce ta karbi hayar gidan ta hannun wani dillali a unguwar.

KARANTA: Hotuna: An tono gawarwaki da littafin mutuwa a makabartar karkashin kasa da aka gina tun lokacin Fir'aun Teti, shekara fiye da 2,500 baya

Matar ta karbi hayar gidan ne akan dubu dari shidda (N600,000) a shekara, a cewar DSP Kiyawa.

An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano
An kama matar dan bindigar Zamfara a cikin masu garkuwa da mutane a Kano
Asali: Twitter

DSP Kiyawa ya kara da cewa matar ta shiga kasuwancin garkuwa da mutane bayan an kashe mijinta wanda shi kansa yana cikin 'yan bindiga da ke satar shanu a jihar Zamfara.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

A watan Oktoba na shekarar 2020 ne rahotanni suka bayyana cewa an yi garkuwa da akalla yara tara a jihar Kano.

Kazalika, an sace Aishatu Aliyu, matar dagacin garin Tsara, Aliyu Muhammad, a cikin watan Oktobar.

A cikin watan Nuwamba ne kuma kafafen yada labarai suka sanar da cewa masu garkuwa da mutane sun sace Babawuro Tofai, kanin ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono.

A wai labarin daban, Legit.ng ta rawaito cewa wasu 'yan bindiga sun kashe wata dattijuwa, Hauwa Umaru, mai shekaru 80 a kauyen Sharu a karamar hukumar Igabi a jihar kaduna.

Kazalika, 'yan bindigar sun kashe jami'an 'yan sanda hudu yayin musayar wuta a hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua.

Duk da hakan, IGP Mohammed Adamu ya jinjinawa tawagar 'yan sanda saboda ta dakile harin da 'yan bindigar suka kai musu yayin da suke kan hayarsu ta komawa Kano bayan kammala wani aiki na musamman.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng