Rundunar 'yan sanda: Mun gano silar mutuwar budurwa a gidan saukar baki na gwamnatin Yobe
- A satin farko na watan Jnairu ne kafafen yada labarai suka wallafa cewa an samu gawar wata matashiyar budurwa a gidan saukar baki na gwamnatin jihat Yobe
- Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa ta kama mutane bakwai da take zarginsu da hannu a mutuwar budurwar
- A cewar sabuwar sanarwa dga rundunar 'yan sanda, budurwar ta mutu ne sakamakon kwayoyin da ta sha
Rundunar 'yan sandan Nigeria ta bayyana cewa kwayoyi ne suka yi sanadiyyar mutuwar wata matashiya mai shekaru 18 a gidan saukar baki na gwamnatin jihar Yobe da ke Damaturu.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe, ASP Dungus Abdul-Kareem, ta ce bincikensu ya tabbatar musu da cewa matashiyar ta kwankwadi miyagun kwayoyi.
A ranar 7 ga watan Janairu ne rundunar 'yan sanda ta kama mutane bakwai bisa zarginsu da hannu a mutuwar matashiyar mai suna Bilkisu Ali, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.
An tsare mutanen a ofishin 'yan sanda yayin da aka mika gawar budurwar asibiti domin gudanar da binciken.
Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa za ta gurfanar da hudu daga cikin mutanen a gaban kotu.
KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria
Kazalika, rundunar ta gargadi jama'a akan su guji yada jita-jita a kan mutuwar matashiyar domin gudun tunzura danginta da abokan arziki.
Legit.ng ta rawaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta sanar da cewa ta kai samame gidan wasu batagari da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Kano.
A cewar rundunar, jami'anta sun samu nasarar cafke mutane hudu a gidan, cikinsu har da wata mace.
Da yake tabbatar da hakan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, ya ce an kama mutanen yayin samamen da jami'an tsaro suka kai gidan da ke kauyenJaba, karamar hukumar Ungogo.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng