Kotu ta yankewa wata mata hukuncin shekaru 43 a gidan kaso kan laifin zagin Sarki

Kotu ta yankewa wata mata hukuncin shekaru 43 a gidan kaso kan laifin zagin Sarki

- Kotu ta yankewa wata mata mumunar hukunci kan kokarin batawa Sarkin kasar suna

- Mutan kasar sun fara gudanar da zanga-zanga kan wannan hukunci

Wata kotun kasar Thailand a ranar Talata ta yankewa wata mata 'yar shekara 87, Anchalee Preelert, hukuncin shekaru 43 a gidan yari kan laifin daura hotuna a yanar gizo da ya batawa Sarkin kasar suna.

Amma daga baya kotun ta rage hukunci zuwa rabin abin aka yanke da farko saboda ta amince da aikata laifin, bisa takardun kotu da jaridar dpa ta gani.

Laifin zagin sarki na da daya daga cikin hukunci mafi tsauri a duniya kuma mutum zai iya shekaru 15 a gidan yari idan aka kama shi da laifin.

An kama Anchalee Preelert, da laifuka da dama na zagin sarki da saba dokokin amfani da yanar gizo ta hanyar daura bidiyoyin da ka iya lalata mutuncin gidan sarauta.

Mutan kasar Thailand sun gudanar da zanga-zanga kan hakan inda suke kira ga canza dokokin kasar zuwa na demokradiyya.

KU KARANTA: Yayinda wa'adin da gwamnati ta bada zai kare yau, har yanzu ba'a hada layuka milyan 29 da NIN ba

Kotu ta yankewa wata mata hukuncin shekaru 43 a gidan kaso kan laifin zagin Sarki
Kotu ta yankewa wata mata hukuncin shekaru 43 a gidan kaso kan laifin zagin Sarki Anchalee Preelert/dpa
Asali: UGC

KU DUBA: An kashe mana Fulani Makiyaya 20 a jihar Neja, Kungiyar Miyetti Allah

A bangare guda, wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yankewa mataimakin kwamishanan yan sanda, Okubo Aboye, da bakanikensa, Niyi Afolabi, hukuncin daurin rai da rai kan laifin amsan motar sata.

Hakazalika Alkalin kotun, John Adeyeye, ya yankewa wasu mutane biyar hukuncin daurin shekaru 5 a Kurkuku kan laifin garkuwa da mutane, TVC ta ruwaito.

Wadannan masu garkuwa da mutane sune Solomon Ayodele Obamoyegun (39), Femi Omiawe (40), Damilola Obamoyegun (20), Bose Sade Ajayi (30), George Lucky (35), Chukwuma Nnamani (22) da Sunday Ogunleye (45).

:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel