An kashe mana Fulani Makiyaya 20 a jihar Neja, Kungiyar Miyetti Allah

An kashe mana Fulani Makiyaya 20 a jihar Neja, Kungiyar Miyetti Allah

- Kungiyar Miyetti Allah ta yi korafi kan yadda ake kashe musu makiyaya a Neja

- Daya daga cikin wadanda abun ya shafa ya bayyana yadda aka kashe mada yara uku

- Wadanda ake zargi da aikata hakan sun karyata rahoton

Kungiyar Makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah (MACBAN) ya bayyana irin kisan gillan da yan banga ke yiwa mambobinsu a karamar hukumar Mashegu na jihar Neja.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Usaini Yusuf Bosso, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Minna, jihar Neja ranar Litinin, Vanguard ta ruwaito.

Alhaji Usaini ya ce cikin yan watanni da suka gabata an kashe mambobinsu ashirin kuma aka babbakasu da wuta a cikin karamar hukumar.

A cewarsa, "mutanen ashirin cikin mambobinmu sun rasa rayukansu a hannun yan bangan karamar hukumar Mashegu, an gona gawawwakinsu."

Wani mutum da yayi ikirarin abun ya shafeshi, Malam Muhammadu Dabo, ya ce an kashe mutum uku cikin yaransa kuma an kona su.

Dabo yace, "Ina daya daga cikin wadanda abun ya shafu saboda an kashe mutum uku cikin yarana kuma aka konasu a gabana a kauyen Tashar Hajiya dake karamar hukumar Mashegu a hannun yan banga."

"Babu abinda na iya domin ceton rayuwar yarana."

KU KARANTA: - Tsohon ministan wasanni na kasa Bala Bello Ka'oje ya rasu yana da shekaru 60

An kashe mana Fulani Makiyaya 20 a jihar Neja, Kungiyar Miyetti Allah
An kashe mana Fulani Makiyaya 20 a jihar Neja, Kungiyar Miyetti Allah
Source: Depositphotos

KU KARANTA: COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

Martani kan hakan, wani babban jami'in yan banga a jihar Neja, Ahmed Gwani, ya bayyana cewa jawabin Miyetti Allah karya ne kuma babu gaskiya a ciki.

A cewarsa, "wannan zargin da suke yi na da girma, kuma kawai suna yi ne domin boye laifukan da suke aikatawa."

"Yan banga mutane ne masu bin doka kuma ba zasu aikata irin wannan ba saboda aikinsu shine kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar Neja ba tare da la'alari da siyasa, addini ko kabilar mutum ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel