Yayinda wa'adin da gwamnati ta bada zai kare yau, har yanzu ba'a hada layuka milyan 29 da NIN ba

Yayinda wa'adin da gwamnati ta bada zai kare yau, har yanzu ba'a hada layuka milyan 29 da NIN ba

- Hukumar NCC ta fitar da wani sabon bayani dangane da alakanta NINs da katinan SIM

- A cewar hukumar, ba za a cire masu amfani da layin sadarwa gaba daya ba sakamakon rashin NIN

- Yau wa'adin da hukumar NCC ta bada zai kare ga yan Najeriya

Kimanin mutane milyan 29 har yanzu basu hada layukan wayansu da lambar katin zama dan kasa NIN ba yayinda wa'adin da gwamnati ta bayar zai kare yau 19 ga Junairu, 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani ma'aikacin gwamnati ya bayyana mata ranar Litinin cewa kimanin layuka milyan 176 aka hada lambar NIN.

Gwamnatin tarayya ta bada wa'adi zuwa ranar 19 ga Junairu ga wadanda ke da lamban NIN dasu hada da lambobin wayansu, yayinda ya bawa wadanda basu mallaki NIN ba tukun ranar 9 ga Febrairu.

Uwa Sulaiman, mai magana da yawun ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, bata amsa tambayar da akayi mata kan makomar layukan da ba'a hada da lambar NIN ba idan wa'adin ya kare.

KU KARANTA: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

Yayinda wa'adin da gwamnati ta bada zai kare yau, har yanzu ba'a hada layuka milyan 29 da NIN ba
Yayinda wa'adin da gwamnati ta bada zai kare yau, har yanzu ba'a hada layuka milyan 29 da NIN ba
Source: UGC

KU KARANTA: An kashe mana Fulani Makiyaya 20 a jihar Neja, Kungiyar Miyetti Allah

Tuni Legit ta ruwaito Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM.

NCC a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga Janairu, ta ce bayanin ya zama dole don kawar da tsoron masu amfani da layuka da sauran jama’a.

An ruwaito mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Adinde yana cewa wani binciken da aka gudanar kwanan nan akwai kusan katinan SIM guda hudu zuwa biyar ga kowane dan Najeriya mai amfani da waya.

Ya ce wannan ya bayyana dalilin bayar da damar hada layukan SIM har guda bakwai zuwa NIN guda daya ta musamman a cikin wata sabuwar hanyar da gwamnatin Najeriya ta bude kwanan nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel