Aiki da Kidnappers: Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai

Aiki da Kidnappers: Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai

- An kama babban jami'in dan sanda da aiki da masu garkuwa da mutane

- Kotu ta yanke mai hukunci mai tsauri fiye da wanda ta yiwa masu garkuwan

- An dade ana zargin akwai hannun jami'an tsaro cikin matsalar rashin tsaro a Najeriya

Wata babbar kotu a jihar Ekiti ta yankewa mataimakin kwamishanan yan sanda, Okubo Aboye, da bakanikensa, Niyi Afolabi, hukuncin daurin rai da rai kan laifin amsan motar sata.

Hakazalika Alkalin kotun, John Adeyeye, ya yankewa wasu mutane biyar hukuncin daurin shekaru 5 a Kurkuku kan laifin garkuwa da mutane, TVC ta ruwaito.

Wadannan masu garkuwa da mutane sune Solomon Ayodele Obamoyegun (39), Femi Omiawe (40), Damilola Obamoyegun (20), Bose Sade Ajayi (30), George Lucky (35), Chukwuma Nnamani (22) da Sunday Ogunleye (45).

Aboye, wanda mataimakin kwamishanan yan sanda ne ACP, da bakanikansa sun saya motar sata daga hannun masu garkuwa da mutane.

Yayinda yanke hukuncin, Alkali Adeyeye yace, "Garkuwa da mutane don amsan kudi abu ne wanda ya zama ruwan dare ba a jihar nan kadai ba, amma a Najeriya gaba daya."

"Da kotun nan ta yi abin kunya idan bata hukunta wadanda ake zargi da hukunci mai tsauri ba."

A karar da aka shigar, "sun aikata laifin ne a Ado Ekiti inda suka yi garkuwa da wani mutum Moses Ajogri kuma suka kwace masa mota kirar Toyota Hilux mai lamba, Lagos APP 509 BK.”

KU KARANTA: Jerin abubuwan da Sarki Ahmad Bamalli ya yi tun da ya hau kan karagar mulki

Aiki da Kidnappers: Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai
Aiki da Kidnappers: Kotu ta yankewa Kwamishanan yan sanda hukunci daurin rai da rai
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: FG tayi amai ta lashe, ta ce bata yarda da bude makarantu a ranar 18 ga Janairu ba

A bangare guda, kungiyar Makiyaya a Najeriya, Miyetti Allah (MACBAN) ya bayyana irin kisan gillan da yan banga ke yiwa mambobinsu a karamar hukumar Mashegu na jihar Neja.

Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Usaini Yusuf Bosso, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Minna, jihar Neja ranar Litinin, Vanguard ta ruwaito.

Alhaji Usaini ya ce cikin yan watanni da suka gabata an kashe mambobinsu ashirin kuma aka babbakasu da wuta a cikin karamar hukumar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel